Real Madrid ta caskara Celtic ta ja ragamar rukuni na shida

An wallafa

Real Madrid ta caskara Celtic da ci 5-1 a wasan karshe a cikin rukuni na shida a Champions League ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Minti na shida da take leda Real ta fara zura kwallo ta hannun Luka Modric a bugun fenariti.

Kungiyar Sifaniya ta kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Rodrygo a minti na 21.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta kara kwallo hudu ta hannun Marco Asensio da Vinicius Junior da kuma Federico Valverde.

Sauran minti shida a tashi daga wasan Celtic ta zare daya ta hannun Jota.

A dayan wasan RB Leipzig ce ta je ta doke Shakhtar 4-0.

Real Madrid ta casa Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni ranar 6 ga watan Satumba a Scotland.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta hada maki 13 a karawa shida a rukuni na shida, sai RB Leipzig mai 12 da Shakhtar Donetsk mai shida da Celtic mai maki biyu.

Real Madrid ce ke rike da Champions League da ta dauka a bara, kuma na 14 jumulla.

Ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba za a raba jadawalin zagaye na biyu na kungiyoyi 16 da za su ci gaba da buga gasar ta Zakarun Turai.

Wasan da Real da Celtic suka fafata a tsakaninsu.

2022/2023

Champions League Laraba 2 ga watan Nuwamba

  • Real Madrid. 5 - 1 Celtic

Champions League Talata 6 ga watan Satumba 

  • Celtic 0 - 3  Real Madrid      

1979/1980

European Cup Laraba 19 ga watan Maris 1980

  • Real Madrid       3 - 0  Celtic

European Cup Laraba 5 ga watan Maris 1980

  • Celtic 2 - 0  Real Madrid      

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde da D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.