Newcastle na son Calvert-Lewin, Douglas Luiz zai koma Juventus

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United na gab da kammala yarjejeniyar daukar dan wasan Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 2, wanda sauran shekara daya kwantiraginsa da Everton ta kare. (Guardian)
Newcastle na son dauko dan wasan baya na Ingila mai taka leda a Wolves Max Kilman, 27. (Telegraph - subscription required)
Wolves ta yi watsi da tayin Kilman daga Newcastle, wadda daman ta tuntubeta kan dan wasan Portugal mai taka leda a kungiyar wato Pedro Neto, 24. (HITC)
Dan wasan Aston Villa, Douglas Luiz, zai koma Juventus, ya kuma shirya domin fara gwajin lafiya a Amurka a mako mai zuwa inda dan wasan tsakiyar mai shekara 26 ke cikin gasar Copa America da Brazil.(Gianluca di Marzio - in Italian)
Manchester City da Manchester United sun nuna sha'awar daukar dan wasa Michael Olise, a kurarren lokaci, bayan ya shirya komawa Bayern Munich da taka leda, duk da hakan kungiyoyin na fatan yin nasara idan dan wasan Faransar mai shekara 22, ya koma Crystal Palace zaman aro a kakar wasa mai zuwa. (Mirror)
Everton na gab da daidaitawa da Manchester United kan mai tsaron gida na Ingila, Jarrad Branthwaite, 21, a baya-bayan nan sun yi watsi da tayin saboda zabtare farashin dan wasan. (Mail)
Everton na tattaunawa da Newcastle kan matashin dan wasan Gambia Yankuba Minteh mai shekara 19. (HITC)
Da alama Newcastle ba ta da ra'ayin dan wasan Liverpool Minteh, wanda ya shafe kakar da ta wuce a zaman aro a Feyenoord karkashin sabon shugaban Liverpool Arne Slot. (Football Insider)
Aston Villa na tuntuba kan dan wasan tsakiya na Sifaniya, mai taka leda a Real Sociedad Brais Mendez, mai shekara 27. (Express)











