Wales ta kori Page a matsayin kocinta

Tsohon ɗan wasan na Wales, Rob Page ya jagoranci Port Vale da Northampton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon ɗan wasan na Wales, Rob Page ya jagoranci Port Vale da Northampton
An wallafa

Wales ta kori kocinta Rob Page bayan shekara uku da rabi yana jagorantar tawagar ƙasar.

Page mai shekara 49 ya jagoranci tawagar ƙasarsa zuwa gasar Kofin Duniya ta farko cikin shekara 64, da kuma zagaye na biyu na gasar ƙasashen Turai ta Euro 2020.

Sai dai kuma gazawar ƙasar ta zuwa Euro 2024, da kuma kasa cin wasa a wasannin sada zumunta na kwanan nan da suka buga da Gibraltar da Slovakia, su ne suka jawo masa korar.

Shugabannin hukumar ƙwallon ƙafa ta Wales (FAW) sun tattauna tsawon mako ɗaya kafin su yanke hukuncin sauya shi.

Page ya fara fuskantar suka ne tun bayan rashin ƙoƙarin da suka yi a gasar Kofin Duniya ta 2022, da kuma rashin nasara a wasannin neman shiga Euro 2024 a hannun Armenia.

"Ina gode wa Rob da bisa aikin da ya yi da Wales cikin shekara bakwai da suka wuce, da farko a matsayin kocin 'yan ƙasa da shekara 21, da kuma Wales," in ji shugaban hukumar FAW Dave Adams.