Hankalin duniya ya karkata kan martanin da Isra'ila za ta mayar wa Iran

H

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Sojojin Isra'ila sun ce kashi 99 na hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa da Iran ta harba an daƙile su ba sukai inda aka harba su ba.

Iran ta ce hare-haren na ramuwar gayya ne kan harin da Isra'ila ta kai wa ofishin jakadancinta da ke Syria makonni biyu baya.

Yaya wannan rikici zai kasance, hakan ya ta'allaka da yadda Isra'ila ta kalli hare-haren da Iran ta kai mata ranar Asabar da daddare.

Ƙasashen da ke yankin da sauran yankunan duniya ciki har da waɗanda ba sa son Iran na ta kiraye-kirayen a kwantar da hankali.

Matsayar Iran ita ce hatin nata ya zama ba za a rama shi ba, ma'ana matsalar ta ƙare daga nan, "ta kuma ja kunnen Isra'ila kan cewa ka da ta yi yunƙurin kai mata hari, idan ba haka ba za ta sake kai mata hari mai ƙarfi da ba za ta iya tare wa ba."

Amma Isra'ila ta sha alwashi "mummunan hari" kuma gwamnati ta kira wannan hari mafi muni a tarihin Isra'ila na baya-bayan nan.

Idan aka dubi yadda ta mayar da martani kan harin da Hamas ta jangoranta na ranar 7 ga watan Oktoba a kudancin Isra'ila cikin gaggawa, da kuma ɗaukar watanni shida da ta yi tana luguden wuta a Gaza.

Da yiwuwar majalisar yaƙin Isra'ila ba za ta kyale wanna harin na kai tsaye ba ya tafi ba tare da mayar da martani ba.

Bayanan bidiyo, Ana jin ƙarar jiniya a faɗin birnin Ƙudus yayin da ake ta ganin wasu abubuwan fashewa a saniyar birnin

Mece ce matsayr Isra'ila yanzu?

Za ta iya sauraren makwabtanta na yankin ta yi abin da ake kira "mai hakuri shi ke dafa dutse" ta ki mayar da martani ta irin hanyar da aka kai mata harin, maimakon haka a ci gaba da yaƙin nesa-nesa tare da ƙawayenta da ke yankin irinsu Hezbollah da ke Labanon da kuma ma'ajiyar makamanta da ke Syria, kamar dai yadda suke yi tsawon shekaru.

Isra'ila za ta iya kai harin samuwa a jere kamar yadda aka yi mata, cikin nutsuwa da kuma hare-haren makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa inda Iran ta riƙa kai mata hari daga wurin a daren jiya.

A

Asalin hoton, Reuters

Hakan kuma zai zama ci gaba da yaƙi a wurin Iran, tunda wannan ne karon farko da Isra'ila ta kai wa Iran hari na kai tsaye, yayin da harinta ya sauka kan waɗanda suke mata yaƙi a yankin.

Ko kuma Isra'ila ta ɗauki mataki na ramuwar gayya cikin muni da zai sake ƙazanta yaƙin, ta faɗaɗa hare-harenta har da sansanoni da kuma wuraren ajiye makamai da cibiyoyin kwamndojin rundunar juyin juya halin Iran.

Ko wanne mataki Isra'ila ta ɗauka Irsan za ta ɗauke shi a matsayin ramuwar gayya.

Abin tambaya a nan shi ne, ko wanne ikicin zai kai ga shigar Amurka, wanda hakan zai zama gagarumin yaƙi tsakanin Iran da dakarun Amurka da ke yankin.

X

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da mambobin Majalisar Tsaro game da harin da aka kai wa Isra'ila a fadar White House

Amurka na da sansanin sojojinta a duka ƙasashe shida na yankin Gulf, haka a Syria da Iraƙi da kuma Jordan.

Wadannan duka za su iya zama inda Iran za su iya hara da makamansu masu cin dogon zango da suka kwashe shekaru suna haɗawa duk da cewa an sa mata takunkumai.

Iran za ta iya yin abin da ta jima tana bazarana a kai idan aka kai mata hari: za ta iya rufe mashigar Hormuz ta hanyar amfani da makamai iri-iri da suka hada da jirage marasa matuka da sauransu, kuma mashigar ita ce hanyar kasuwanci kashi ɗaya cikin uku na man da ake samarwa a duniya.

Wannan zai iya zama abu mara dadi da zai iya jefa Amurka cikin yaƙin Gabas ta Tsakiya, wanda gwamnatoci da yawa a duniya ke aiki dare da rana domin ganin hakan bai faru ba.