Richarlison ba zai buga wa Tottenham wasan firimiya na farko ba

Asalin hoton, BBC Sport
Sabon dan wasan da Tottenham ta saya, Richarlison ba zai buga wasan Firimiya na farko ba a kakar bana da za a fara, bayan da aka dakatar da shi wasa daya bayan faruwar wani lamari a watan Mayu.
Dan wasan gaban mai shekara 25, ya jefa abin tartsatsin wuta cikin magoya baya a wasan da tsohuwar kungiyarsa Everton ta sami nasara da ci 1-0 kan Chelsea a filin wasa na Goodison Park.
Bayan dakatar da shi buga wasa daya an kuma ci tarar sa yuro 25,000.
Richarlison wanda dan asalin kasar Brasil ne, ya amsa laifinsa da cewa hakan bai kamata ba.
Abin da dan wasan ya aikata ya saba ka’ida ta yanda ake son dan wasa ya kasance mai kyawun hali.
Richarlison ya dauki abin tartsatsin wutar wanda magoya baya suka jefa cikin fili a lokacin da yake murnar cin kwallon da kungiyarsa ta yi nasara kan ‘yan wasan Thomas Tuchel, wanda kuma ya taimakawa kungiyar ci gaba da zama a gasar firimiya.
A kakar wasa da aka kamala, saura kadan kungiyar ta fada gasar championship, inda kwallaye 10 da Richarlison din ya ci ya taimaka mata ci gaba da zama a gasar ta Firimiya.
A farkon watan Yuli ne, aka sanar da cewa dan wasan ya rattaba hannu kan kwantiragi kaka biyar da Tottenham.












