PSG ta raba gari da Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain ta sanar da ta raba gari da Mauricio Pochettino, bayan wata 18 yana gudanar da aikin kociyan kungiyar.
Tun bayan wata daya ake sa ran tsohon wanda ya horar da Tottenham, mai shekara 50, zai bar PSG, amma sai yanzu aka tabbatar da tafiyarsa.
Ana sa ran tsohon kociyan Nice, Christophe Galtier ne zai maye gurbin dan kasar Argentina.
Pochettino ya bar PSG, bayan da ya ja ragamar kungiyar ta lashe French League na kakar da aka kammala na 10 jumulla, kuma na farko da ya dauka a matakinsa na koci.
Tsohon mai tsaron bayan PSG, ya ja ragamar dukkan wasa a kakar da wuce a lik ba tare da an doke kungiyar ba a gida, wanda ya yi nasara a wasa 16 daga 19.
PSG ta samu damar lashe babban kofin gasar Faransa, amma an yi waje da ita a zagayen kungiyoyi 16 a Champions League, kofin da Real Madrid ta dauka..

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ce ta yi waje da PSG, wadda ke kishirwar lashe babban kofin Zakarun Turai a karon farko, hakan ne ya sa alamar tambaya kan makomar Pochettino a kungiyar ta Faransa.
PSG wadda ta kai wasan daf da karshe a 2021 da buga karawar karshe a 2020, ta kasa taka rawar gani a kakar da ta wuce da aka sa ran za ta iya daukar kofin.
Tottenham ta sallami Pochettino a Nuwambar 2019, bayan kaka biyar a kungiyar, wata daya tsakani da ya kai ta wasan karshe a Champions League.
Bayan da ya karbi aikin horar da PSG a Janairun bara, kungiyar ta karkare a mataki na biyu a Ligue 1, sannan Manchester City ta doke ta a wasan daf da karshe a Champions League.
Sai dai PSG ta lashe Coupe de France da kuma Trophee des Champions, wadanda sune na farko da Pochettino ya dauka a matakin mai horarwa.
Tsohon mai tsaron bayan tawagar Argentina, ya fara aikin koci a Espanyol daga nan ya koma Southampton, sannan Tottenham ta dauke shi a watan Mayun 2014.












