Buhari ya umarci ministocinsa su ci gaba da aiki har jajiberin barin gwamnati

Buhari da ministocinsa
Bayanan hoto, An yi tsammanin Buhari zai rushe majalisar ministocinsa yayin zamanta na ƙarshe ranar Laraba
An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya umarci ministocinsa su ci gaba da aiki har zuwa jajiberin ranar sauka daga mulki.

An yi ta hasashen shugaban zai rushe majalisar ministocin tasa a yau Laraba yayin zaman ƙarshe da ya jagoranta bayan shafe shekara takwas a kan mulki.

Sai dai shugaban ya umarce su da su ci gaba da aiki har zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu, kamar yadda Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu za a rantsar da shugaba mai jiran gado Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.

An gudanar da zaman ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Mahalarta taron sun ƙunshi Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo da dukkanin ministoci 44 na gwamnati da kuma ƙananan ministoci.

An gabatar da jawabai na yadda al'amura suka kasance tsawon mulkin shugaban ƙasar da kuma jawaban ban-kwana.

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya hau kan mulki bayan doke tsohon shugaban ƙasa mai ci Goodluck Jonathan.

A lokacin da ya hau mulki, Buhari ya yi alƙawarin murƙushe rashin tsaro ta hanyar kawar da ƙungiyar Boko Haram, da yaƙi da rashawa da kuma yaƙi da talauci.

Muhammadu Buhari ya zama shugaban Najeriya ne a 2015 bayan kayar da shugaba Jonathan

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Muhammadu Buhari ya zama shugaban Najeriya a 2015 bayan kayar da Shugaba Jonathan

Abubuwan da aka gudanar a taron

Shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari yake karɓar rahoton kwamatin gyara harkokin lafiya daga Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo

An fara ne da amincewa ko daddalewa kan ƙudirorin da majalisar ta tattauna a kansu a zaman da ta yi uku a baya.

Jim kaɗan bayan fara taron, Buhari ya rantsar da kwamashinoni bakwai na hukumar tattarawa da nemowa da kuma raba kuɗin shiga ta ƙasa wato Revenue, Mobilization, Allocation and Fiscal Commission (RMAFC).

Kazalika, Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya miƙa wa shugaban ƙasa rahoton kwamatin inganta harkokin lafiya a Najeriya.

"Mahalaata taron na cikin yanayi na sosa rai musamman saboda ministoci da yawa sun shafe shekara takwas tare da Shugaba Buhari a gwamnatin," a cewar wakilin BBC Hausa Haruna Shehu Tangaza wanda ke fadar shugaban ƙasar.

Rahotanni sun ruwaito cewa wasu daga cikin ministoci sun kwashe kayansu daga ofis a shirye-shiryen miƙa ragama.

Bola Tinubu ya lashe zaɓen da aka gudanar a watan Fabarairu ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki bayan ya kayar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, wanda ya zo na biyu.

Masana na ganin akwai abubuwa da dama za a tuna gwamnatin ta Shugaba Buhari da su na nasara da kuma akasin haka bayan tafiyarta.

Duk da cewa wasu na ganin an samu nasara a ɓangaren samar da kayan ci gaba amma al'umma na kokawa kan rashin ingancin tattalin arziƙi da taɓarɓarewar tsaro.

Ga wasu hotunan yadda zaman ƙarshe na majalisar ya kasance:

Shugaba Muhammadu Buhari da ministcoinsa

Asalin hoton, State House

Shugaba Muhammadu Buhari da ministcoinsa

Asalin hoton, State House

Shugaba Muhammadu Buhari da ministcoinsa

Asalin hoton, State House