Sallar Idin Buhari ta ƙarshe a kan mulki

Buhari eid

Asalin hoton, BUHARI SALLAU/FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari tare da muƙarraban gwamnatinsa a Masallacin Barikin Mambilla lokacin Idin Ƙaramar Salla
An wallafa

Hausawa kan ce Salla mai yawan baya!

Ga dukkan alamu, wannan zance ya fi zama gaskiya, ga shugaban da ya yi Idinsa na ƙarshe a kan karagar mulkin Najeriya.

Bikin Ƙaramar Salla da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a Abuja, zai kasance ɗaya daga cikin muhimman lokuta a tarihin rayuwarsa.

Ya zo ne a lokacin da shugaban na Najeriya ke tattara nasa-i-nasa daga fadar mulki ta Dutsen Aso, kafin ya miƙa harkokin shugabanci ga magajinsa nan da mako biyar.

Yana dai fatan komawa can nesa da Abuja, mai cike da ƙalubale da matsalolin mulkin ‘yan Najeriya kimanin miliyan 200 zuwa cikin iyali a gidansa na Daura.

Wani wuri da shi ma yake da tarihi, idan ana maganar bukukuwan sallar idi guda 17 da Buhari ya gani a zamanin mulkinsa na tsawon shekara takwas.

Buhari eid

Asalin hoton, BUHARI SALLAU/FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yana fatan nisantar Abuja bayan ya miƙa mulki hannun magajinsa nan da 'yan makonni

Jawabin bikin sallar idin Buhari na ƙarshe dai, ya saɓa da na sallar idinsa na farko.

A idin farko, jawabin cike yake da alƙawurran shugabancin da zai gyara kura-kuran masu mulki na baya. Neman ci gaba da goyon baya da nuna fahimta da kuma haƙuri daga 'yan ƙasa.

Akwai ƙudurin fifita aiki mai nagarta kuma cikin tsanaki, maimakon tafiyar sauri da wasu suka fara ƙosawa suka ga an yi. Sai kuma alƙawarin karya lagon taɓarɓarewar tsaro da cin hanci da kuma ƙarancin ayyukan raya ƙasa.

Sallar Idin Buhari ta watan Yulin 2015, ta zo ne lokacin da Najeriya ke tsakiyar fama da rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram, wadda ta zafafa hare-hare kan mazauna ƙauyuka da garuruwa har ma da birane.

Hasali ma dai sallar ta zo ne mako biyu bayan wani mummunan harin ƙunar bakin wake da mayaƙan ƙungiyar suka kai Zabarmari, kusa da Maiduguri.

Inda aka kashe mutane da yawa ciki har da soja ɗaya a harin, wanda mayakan Boko Haram suka riƙa buɗe wuta, wasu ‘yan mata guda shida kuma suka tayar da bama-baman da suka yi jigida da su.

A cikinsu wata ta yi yunƙurin kutsawa wani masallaci, ana sallar tarawi.

Buhari eid

Asalin hoton, BORNO STATE GOVT

Bayanan hoto, Hare-haren bam da ƙungiyar Boko Haram ke kai wa cikin biranen arewacin Najeriya kamar wannan a farkon shekara ta 2020 sun ƙara raguwa sosai

Kwana biyu kafin nan, Boko Haram ta kai wasu hare-hare a kan wasu ƙauyuka cikin ƙaramar hukumar Kukawa da suka yi sanadin kashe masallata kusan 100.

.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Lokacin da aka yi sallah ƙarƙashin kullen korona mutane da dama ba su gudanar da bikin sallar ba kamar yadda suka saba kafin annobar

A Idinsa na ƙarshe a kan mulki kuwa, jawabin Buhari da ya fi jan hankali shi ne wanda ya yi wa rukunin wasu shugabannin al'ummomin Abuja, lokacin da suka kai masa ziyarar barka da salla.

Jawabi ne da cike da tsokacin rayuwarsa kafin, da kuma bayan mulki.

Ya dai nanata bayanin da ya sha yi cewa zai tafi nesa da Abuja.

Buhari eid

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Shugaba Buhari a gonarsa ta Daura

Kuma ya nemi afuwa daga waɗanda ya ɓatawa a tsawon shekara takwas.

Duk da yake, har a wannan bikin idin Ƙaramar Sallah na 2023, kamar na 2015, Najeriya tana fama da matsalolin tsaro, musamman na 'yan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar

Amma wani muhimmin bambanci shi ne, yadda ake ƙara mantawa da ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-baya da ta yi ƙaurin suna a duniya, wato Boko Haram.

A wannan karo dai ko ba komai, dogayen layukan masu ibada da suka riƙa fuskantar binciken jami’an tsaro kafin shiga masallatan Juma'a da na idi, sun daɗe da ɓacewa.

Buhari eid

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto, Ban da shanu, Shugaba Buhari yana kuma kiwo wasu dabbobi kamar dawakai
.

Asalin hoton, MBuhari

Juma'a ga alama, muhimmiyar rana ce a tarihin mulkin shugaban mai barin gado.

Muhammadu Buhari ya fara Sallar Idinsa ta farko a kan mulki, ranar Juma’a 17 ga watan Yulin 2015 a filin Idi na Abuja, ƙasa da wata biyu bayan rantsar da shi.

Kuma ya kammala Sallar Idinsa ta 17 karon ƙarshe a kan mulki, a Barikin Mambila cikin Abuja ranar Juma’a 21 ga watan Afrilun 2023.

.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bikin Sallar Idi, kamar wannan na Ƙaramar Sallah da muke ciki, ga ma’aikata da manyan jami’an gwamnati, lokaci ne na samun sararawa daga ayyukan ofis.

Shugaba Muhammadu Buhari ya riƙa amfani da lokacin wajen sada zumunci tsakanin iyalai da dangi.

Ya ƙara buɗe ƙofar karɓar masu ziyara da ke zuwa gaisuwa da fatan alheri da kuma taya shi murnar an yi salla lafiya.

Buhari Eid

Asalin hoton, BUHARI SALLAU/FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaba Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattijai da Zainab Marwa-Abubakar a lokacin bikin Ƙaramar Salla

A duk lokutan bukukuwan Sallar Idi, akan ga manyan jami’an gwamnati ciki har da mataimakinsa Yemi Osinbajo da ministoci.

Haka ma gwamnoni da 'yan majalisa da ƙusoshin jam’iyya mai mulki da sarakuna da shugabannin al’umma da na addinai suna tururuwar zuwa gaisuwa a fadar Aso ko kuma a Masarautar Daura.

g

Asalin hoton, Buhari Sallau

A irin wannan lokaci akan ga hotunan shugaban cikin 'ya'ya da jikoki da sauran makusanta da kan je gaisuwar salla.

An lura cewa akasari Shugaba Buhari ya fi yin shagulgulan Ƙaramar Salla a Abuja, a lokacin bikin Babbar Salla kuma yakan je mahaifarsa ne wato Daura.

Buhari eid

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Bayanan hoto, Bikin Salla, ga alama lokaci ne ga shugaban ƙasar mai son yara, na gamuwa da jikokinsa maza da mata

Yakan halarci masallaci, sannan bayan an sauko daga idi ya saba yin tattaki a tsakiyar al'ummar da kan yi dandazo suna kai gaisuwa da kuma kai caffa.

Sai dai a shekara ta 2020, Buhari yanka ragon sallarsa ne a Abuja, saboda bai je Daura ba, dalilin cutar korona.

Hy

Asalin hoton, HT

Alaƙar Buhari da Sarakuna

Sallar Idi dai, bikin shekara-shekara ne da kan zo da batun komawa ga al'ada da kuma gargajiyar al'ummar Hausawa.

Ba abin mamaki ba ne ganin babbar alaƙar da shugaban ya gina tsakaninsa da sarakuna a faɗin Najeriya, kasancewarsa mutumin Daura. Mashahuriyar Masarauta mai daɗaɗɗen tarihi a cikin Hausa bakwai.

Muhammadu Buhari ya sha nanata muhimmiyar gudunmawar da sarakuna ke iya bai wa shugabannin ƙasa kamar sa wajen inganta ayyukan tattara bayanan sirri a yankuna da masarautunsu don magance babbar matsalar da ta addabi Najeriya a zamanin mulkinsa, wato ƙalubalen tsaro.

Buhari eid

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Bayanan hoto, Shugaba Buhari da sarakunan Najeriya yayin wani taro a kan tsarin iyali a Musulunci cikin watan Fabrairun 2020

Kyautar sarauta da aka gani an bai wa Shugaba Buhari ta ƙarshe a bainar jama'a, ita ce wadda Sarki Aminu Ado Bayero ya miƙa masa a watan Janairun 2023, wani zungureren ƙaho.

Rahotanni dai sun ce ƙahon wani maƙunshin kyauta ne na karramawa kuma yana ƙunshe ne da wata babbar rigar sarakuna.

Buhari eid

Asalin hoton, BASHIR AHMED/FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yayin wata ziyara da ya kai Sarki Aminu a fadar da ke Kano cikin watan Janairun 2023

Sarakuna sun sha karɓar sa a ziyarar da yake kai wa fadarsu zamanin mulkinsa, ga alama shi ma ya buɗe ƙofar fadarsa ga masu sarautar da suka sha zuwa ziyara daga faɗin Najeriya.

y

Asalin hoton, Buhari

Mai yiwuwa wannan ba abin mamaki ba ne, ga mutumin da ke riƙe da sarautar 'Bayajiddan Daura'.

A bikin Babbar Salla cikin 2021, Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk ya sake gwangwaje Buharin da iyalinsa, da wata sabuwar sarauta, ta hanyar naɗa babban ɗansa namiji, Yusuf Buhari, matsayin Talban Daura, kuma Hakimin Ƙwasarawa.

g

Asalin hoton, BASHIR AHMED

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Ahmad Lawan a garin Daura don naɗin sarautar Talban Daura.

Ban da aminta, Shugaba Buhari ya haɗa surukunta da sarakuna kamar na Kano.

A cikin watan Agustan 2021 ne, aka yi ƙasaitaccen bikin da a nan kusa ba a ga irinsa ba cikin sabuwar Masarautar Bichi, kai ƙari wallahi ma har a babbar Masarautar Kano.

Lokacin da aka ɗaura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero, ɗiyar Sarkin Bichi, Mai martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Yayin bikin, garin Bichi da ke wajen birnin Kano, ya shaida manyan baƙi da suka hadar da jami'an gwamnati da sarakuna da ɗumbin mutane masu fatan alheri.

Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ya ga saukar jiragen sama masu tarin yawa.

Buhari eid

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Bayanan hoto, Shugaba Buhari tare da Sarkin Daura Faruƙ Umar Faruƙ

Babu daɗewa kuma a cikin wannan shekara, Sarkin Daura ya ɗaga darajar ƙauyen Dumurkol, mahaifar Buhari zuwa garin Hakimi.

Shekara ɗaya kafin nan cikin watan Disamban 2020 a lokacin wata ziyarar hutu ta tsawon mako ɗaya a Masarautar Daura, Buhari ya samu ƙasaitacciyar tarba da wata kyautar sarakuna ta kilin doki, taka-haye da takobin yaƙi.

An shiga yanayin damuwa

Cikin ƙalubalen da alaƙar Shugaba Buhari da sarakuna ta fuskanta har da ka-ce-na-cen da aka fuskanta a lokacin da gwamnatin jihar ta tuɓe sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sanusi na II.

j

Asalin hoton, Ibrand

Sai da ta kai ga fadar Shugaba Buhari fitar da sanarwa tana musanta duk wani hannu a dambarwar tuɓe Muhammadu Sanusi daga sarautar Kano.

A tsawon mulkinsa na shekara takwas, Shugaba Buhari ya sha ganawa da shugabancin Majalisar Sarakuna ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da Ooni na Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

Majalisar dai ta shafe tsawon lokaci tana gwagwarmayar ganin tsarin mulkin Najeriya ya martaba sarakuna tare da ba su ikon da ya kamaci matsayinsu a ƙasar.

Sai dai, fafutukar Majalisar Sarakunan ta ganin an mayar wa masu sarauta ikonsu cikin tsarin mulkin Najeriya, a tsawon shekara takwas na mulkin Buhari, a iya cewa, ba ta dace da nasara ba.