Buhari zai rantsar da sabbin ministocinsa

ministocin Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

An wallafa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai rantsar da majalisar ministocinsa, don fara aiki gadan-gadan a wa'adi na biyu na mulkinsa, bayan lashen zaben watan Fabrairu.

Sabbin ministocin 43 da majalisar dattawa ta tantance sun hada da mutum 12 da aka yi wa'adin farko da su, da kuma mata guda bakwai.

Ministocin su ne za su taimaka wa Buhari wajen tsarawa da aiwatar da alkawurran zabe da ya yi wa 'yan Najeriya, a matsayinta na kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka.

Ana sa ran shugaban zai sanar da ma'aikatar da kowanne minista zai yi aiki.

Wannan na zuwa bayan shugaban ya jagoranci taron bitar sanin makamar aiki ga ministocinsa a ranar Talata.

Ana sa ran bayan bikin rantsar da ministocin, shugaban kuma zai kaddamar da majalisar zartarwa ta hanyar jagorantar zaman farko da sabbin ministocin nasa.

Kusan wata uku kenan aka shafe ana tafiyar da gwamnati ba ministoci tun rantsar da Buhari a ranar 29 ga Mayu.

Ko da yake, a wa'adin mulkinsa na farko, shugaban bai nada ministoci ba sai bayan kusan watanni shida da karbar ragamar mulkin kasar.

Mata bakwai daga cikin sabbin ministocinsa sun hada da Sharon Ikeazor daga Anambra da Ambasada Maryam Katagum daga Bauchi da Gbemi Saraki daga Kwara da Ramatu Tijani daga Kogi da Pauline Tallen daga Filato da Zainab Ahmed daga Kaduna sai kuma Sadiya Farouq daga Zamfara.

Sauran sun hada da:

Ministocin Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe

Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom

Alhaji Sabo Nanono - Kano

Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun

George Akume - tsohon gwamnan - Benue

Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa

Sanata Olorunnibe Mamora - Legas

Sunday Dare - Oyo

Festus Keyamo - Delta

Sanata Tayo Alasoadura - Ondo

Mustapha Buba Jedi Agba -

Olamilekan Adegbite - Ogun

Mohammed Dangyadi - Sokoto

Abubakar Aliyu - Yobe

Sale Mamman - Taraba

Muhammed Mamood - Kaduna

Uce Ogar - Abia

Emeka Nwajuiba - Imo

Akpa Udo

Clement Abam

Zubair Dada

Adeniyi Adebayo - Ekiti

Mohammed Abdullahi

Osagie Ehenere

Bashir Salihi Magashi - Kano

Tsoffin ministocin da suka dawo

Ministocin Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Babatunde Fashola - Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje

Rotimi Amaechi - Tsohon Ministan Sufuri

Ogbonnaya Onu - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha

Adamu Adamu - Tsohon Ministan Ilimi

Sanata Chris Ngige - Tsohon Ministan Kwadago H

Hadi Sirika - Tsohon Karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama

Zainab Ahmad - Tsohuwar Ministar Kudi

Lai Mohammed - Tsohon Ministan Watsa Labarai

Musa Bello - Tsohon Minsitan Abuja

Abubakar Malami - Tsohon Ministan Shari'a

Sulaiman Adamu - Tsohon ministan ruwa

Baba Shehuri - Borno

Sharhin Masana

Tun bayan kawo karshen wa'adin mulkinsa na farko, Shugaba Buhari ya yi ikirarin cewa ministocinsa sun taka rawar gani, kuma shi ne dalilin da ya sa ya ci gaba da tafiya da su har tsawon shekara uku da rabi wato zuwa karshen wa'adinsa ba tare da ya sauya su ba.

Buhari ya yi ikirarin cewa sun samu nasarar cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe, kuma ministocin sun taka rawa ga samun nasarar.

Dakta Abubakar Kari, mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya ya shaida wa BBC cewa akwai ministoci da dama da ba su taka rawar gani ba, wadanda ya ce "ba su cancanta a sake tafiya da su ba."

"Idan ka yi maganar ma'aikatu kamar na lafiya da sadarwa da na jiragen sama, ayyukan da ministocin suka yi bai gamsar da 'yan Najeriya ba."

"Sun kuma yi alkawura da dama kamar na magance matsalar wuta da kuma hanyoyi da suka kasa aiwatarwa," a cewarsa.

Dakta Kari ya jaddada cewa wadannan abubuwan da ya lissafo, ba wai yana nufin cewa ba su tabuka komai ba, "mutane dai ba su ga ayyukan da suka yi tunanin za a yi ba."

Masana harkokin tsaro da dama irinsu Malam Kabiru Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro - musamman a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.

Sai dai sun nuna gazawar shugaban wajen shawo kan matsalolin 'yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa a jihohin arewa maso yammaci, matsalolin da suka yi kamari a yanzu.