Chelsea za ta dauki kociyan Leicester City Maresca

Asalin hoton, Getty Images
Wasu rahotanni na cewa Chelsea za ta tattaunawa da mai horar da Leicester, Enzo Maresca, domin ya zama sabon kociyanta.
Ɗan kasar Italiya, ya yiwa Pep Guardiola mataimaki a Manchester City, wanda ya ja ragamar Leicester City zuwa Premier League da lashe Championship a bana.
A bara ne ƙungiyar King Power ta bar babbar gasar tamaula ta Ingila tare da Southampton da kuma Leeds United.
Chelsea ta yaba da salon yadda kociyan ke horar da tamaula, domin ya maye gurbin Mauricio Pochettino, wanda ya yi aikin kaka daya a Stamford Bridge.
Wasu rahotanni na cewar Chelsea ta nemi izinin tattaunawa da Marresca daga Leicester City, wadda take fatan yiwa tayin yarjejeniyar £10m.
Haka kuma cikin wadanda Chelsea ke fatan tuntuba har da na Brentford, Thomas Frank da Kieran McKenna, wanda ya yi na biyu a Championship a bana da kai Ipswich gasar Premier ta badi.
Chelsea, wadda ta fara kakar bana da ƙalubale ta kare a mataki na shida a teburin Premier League, bayan kammala kakar bana ranar Lahadi 19 ga watan Mayu.
To sai dai Chelsea za ta buga wasan cike gurbin shiga Europa Conference League, bayan da Manchester United ta lashe FA Cup ranar Asabar.
United ta yi nasara a kan Manchester City da cin 2-1, sannan ta lashe kofin da ya ba ta damar buga Europa League a badi kai tsaye.
United ta kare a mataki na takwas a teburin Premier League, gurbin da ba zai ba ta damar wakiltar Ingila daga gasar zakarun Turai a badi ba.
Amma ɗaukar FA Cup da ta yi ranar Asabar kuma na 13 jimilla, ya ba ta damar shiga gasar Europa League kai tsaye ta badi.
Newcastle United, wadda ta kare a mataki na bakwai ɗin teburi ba ta samu damar shiga gasar zakarun Turai ta badi ba.











