PSG ta sauya shawara kan Mbappe, Arsenal da Liverpool na harin Ait-Nouri

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa Paris St-Germain ta yi wa Kylian Mbappe tayin sabon kwantiragi da ya kai albashin yuro miliyan 100 a kaka domin shawo kan ɗan Faransan ya ci gaba da zama. (AS daga Mirror)
Arsenal da Liverpool na son sayen dan baya na gefen hagu na Wolves, Rayan Ait-Nouri ɗan Algeria mai shekara 22 . (Football Transfers)
Liverpool ɗin kuma tana son riƙe ɗan wasanta na tsakiya Thiago Alcantara amma kuma ɗan Sifaniyan mai shekara 32 na ɗaukar hankalin ƙungiyar Flamengo ta Brazil da kuma Al-Ettifaq ta Saudiyya. (Teamtalk)
Newcastle za ta sake nazari a kan shiryeshiryenta na cefane na watan nana na Janairu a lokacin wani taro na musamman a makon nan sakamakon raunin da ɗan wasanta na tsakiya Joelinton, na Brazil ya ji. (Guardian)
Chelsea ba ta da wata sha'awa ta ɗan wasan gaba na Sporting CP da Sweden Viktor Gyokeres duk da rahotannin da ake yaɗawa na cewa ta taya shi fam miliyan 73. (Football London)
Brentford ta cimma yarjejeniya ta baka da Tottenham domin bai wa ƙungiyar ta arewacin London aron ɗan bayanta Sergio Reguilon, na Sifaniya, amma kuma babu sharaɗin sayenshi dindindin. (Fabrizio Romano ta X)
Manchester United na harin ɗan gaban Bologna Joshua Zirkzee na Holland mai shekara 22 a bazara. (Florian Plettenberg daga X)
Wolves na tunanin zawarcin ɗan gaban Albania Armando Broja, mai shekara 22, wanda makomarsa za ta kasance kan ko Chelsea za ta sayi sabon ɗan gaba a watan nan. (Guardian)
Arsenal na tattaunawa da Besiktas kan cinikin ɗan baya Cedric Soares na Portugal mai shekara 32 . (Mail)
Ɗan gaban Burkina Faso Bertrand Traore da ɗan baya Calum Chambers, ɗan Ingila na jan hankalin ƙungiyoyin Turai, bayan da Aston Villa ta ce musu za su iya tafiya a watan Janairu. (Football Insider)
Jose Mourinho ka iya komawa tsohuwar ƙungiyarsa Porto bayan da Roma ta sallame shi ranar Talata. (Express)











