Real Madrid za ta kara da Atletico a Copa del Rey zagayen ƴan 16

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Talata za a ci gaba da wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar Copa del Rey ta Sifaniya.

Za a buga karawa uku ranar Talata, domin tantance wadanda za su kai zagayen quarter finals.

Za a fara wasa tsakanin Getafe da Sevilla a filin wasa na Coliseum Alfonso Perez ranar Talata.

Daya karawar za a fafata ne tsakanin Athletic Bilbao da Deportivo Alaves da za su kece raini a filin Estadio San Mames.

Wasa na uku kuwa za a yi ne a filin Heliodoro Rodriguez tsakanin CD Tenerife da Real Mallorca.

Ranar Laraba ma karawa uku za a yi tsakanin Valencia da Celta de Vigo a filin wasa na Estadio Mestalla.

Real Sociedad za ta ziyarci filin wasa na El Sadar, domin fafatawa da Osasuna, yayin da za a barje gumu tsakanin Girona da Rayo Vallecano a Montilivi.

Za a kammala da karawa biyu ranar Alhamis tsakanin Unionistas Salamanca da Barcelona da za su kara a Estadio Municipal da kuma wanda Real Madrid za ta je gidan Atletico Madrid.

Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, sai Athletic Bilbao mai 23 da Real Madrid mai 20 da kuma Atletico mai 10.

Jerin wasannin kungiyoyi 16 a Copa del Rey

Ranar Talata 16 ga watan Janairun 2024

  • Getafe da Sevilla
  • Athletic de Bilbao da Deportivo Alaves
  • CD Tenerife da Real Mallorca

Ranar Laraba 17 ga watan Janairun 2024

  • Valencia da Celta de Vigo
  • Osasuna da Real Sociedad
  • Girona da Rayo Vallecano

Ranar Alhamis 18 ga watan Janairun 2024

  • Unionistas Salamanca da Barcelona Estadio Municipal
  • Atletico de Madrid da Real Madrid