Barcelona na harin Kane, Chelsea na zawarcin Adam Wharton

Asalin hoton, Getty Image
Barcelona na kan gaba wajen zarwarcin ɗan wasan gaban Igila da Bayern Munich Harry Kane, yayin da Chelsea ke zawarcin Adam Wharton, sai Juventus da ta dakatar da aniyarta siyen ɗan wasa Kenan Yildiz.
Barcelona matsa lamba kan ɗan wansan gaban Bayern Munich da Ingila Harry Kane mai shekaru 32, a matsayin zaɓin su, don maye gurbin ɗan wasan gabansu na ƙasar Poland Robert Lewandowski mai shekaru 37, a kakar wasa mai zuwa, wanda ake hasashen za a iya siyen sa kan fam miliyan hamsin da bakwai (£57m) kamar yadda yake a wani sashe na kwantaragin sa da Beryern Munich. (Guardian)
Ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekaru 21, na cikin jerin ƴan wasa da Chelsea ke fatan siye, idan aka fara ɓude siyen ƴan wasa a watan Janeru. (Teamtalk)
Tsohon ɗan wasan gaba na Tottenham Son Heung-min, mai shekaru 33, ya ce ba zai bar Los Angeles FC ba, a matsayin ɗan wasan aro a watan Janeru mai zuwa ba, sakamakon kamala wasannin kakar gasar. (Evening Standard)
Juventus na fatan ganin ta yi nasarar jan hankalin, mai tsaron ragar Faransa Mike Maignan, don koma wa ƙungiyar ya ci gaba da taka leda, idan kwantaraginsa da AC MIlan ta ƙare, a kakar wasaanin da ake ciki, haka itama Chelsea na zawarcin ɗan wasan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Chelsea ba ta yi wani yunƙuri ba kan ɗan wasan gaban Real Madrid da Brazil Rodrygo ba, mai shekaru 24, da ke da sha'awar zuwa Manchester City da Tottenham. (Fabrizio Romano)
Juventus ta gaza cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba na Turkiya mai shekaru 20 Kenan Yildiz - wanda ake hasasshen zai iya koma wa Arsenal, ko Chelsea, da Real Madrid, don sabunta kwantaraginsa, bayan da ɓangarorin suka dakatar da ci gaba da tattaunawa. (Gazzetta dello Sport - in Italian).
Real Madrid na tattaunawa ta ƙarshe kan siyen ɗan wasan Lyon, kan siyen ɗan wasan ƙasar Brazil mai shekaru 19, don taka leda a ƙungiyar a Faransa a matsayin aro a watan Janeru. (Globo Esporte - in Portuguese).
Napoli da Leeds na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Ingila England Kobbie Mainoo, 20, duk da cewa Mancherter ba za ta barshi ya tafi a msatyin aro ba, idan za su sami wanda zai maye gurbinsa. (Teamtalk)
Ɗan wasan baya na Denmark Andreas Christensen, 29, na son ya ci gaba da taka leda a Barcelona, amma sai dai ya ce yana da wani shirin idan ƙungiyar ta sa taƙi sabunta masa kwantaraginsa, nan da kakar wasa mai zuwa. (Tipsbladet - in Danish)
tsohon dan wasan baya na Croatia Slaven Bilic ya ce sauran ƙirisa ya sake dawo mai horar da ƙungiyar kwallon ƙafa ta West Ham, kafiin su sauya ra'ayinsu su ɗauki Nuno Espirito Santo. (Talksport).









