Man United na son Goncalves, Barca ta raba kafa kan Rashford

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na son Pedro Goncalves na Sporting ya maye gurbin Bruno Fernandes a Old Trafford, Bayern Munich na zawarcin Eberechi Eze na Crystal Palace yayin da Manchester City ke shirin neman dan wasan Lyon Rayan Cherki.
Manchester United na sha'awar sayen danwasan tsakiya na Portugal da Sporting Pedro Goncalves, mai shekara 26, a matsayin wanda zai maye gurbin Bruno Fernandes, mai shekara 30, idan ya koma Saudiyya a bazara. (Sunday Mirror)
Bayern Munich na sha'awar sayen danwasan tsakiya na Ingila da Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 26. (Football Insider)
Crystal Palace na son Eze ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da su duk da sha'awar da sauran kungiyoyin Premier kamar Arsenal da Tottenham da kuma Manchester City ke nunawa kansa. (The I)
Danwasan Liverpool dan kasar Holland Cody Gakpo, mai shekara 26, da kuma dan kasar Japan Kaoru Mitoma na Brighton, mai shekara 28, suma suna cikin jerin wadanda Bayern Munich ke son dauka. (Christian Falk)
Danwasan gaban Brazil Rodrygo, mai shekara 24, ya shaida wa Real Madrid cewa yana son ci gaba da zama a kungiyar duk da sha'awar da kungiyoyin Premier daban-daban ke nunawa kansa. (Marca Spanish)
Manchester City za ta gabatar da tayin farko kan danwasan tsakiya na Lyon da Faransa Rayan Cherki, mai shekara 21 a wannan makon. (Fabrizio Romano)
Barcelona za ta karfafa neman da take yi wa danwasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford mai shekara 27 ne idan bata cimma matsaya da dan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 28 na Liverpool ba. (Mundo Deportivo)
Tottenham na duba yiwuwar rike danwasan gaban Faransa Mathys Tel, mai shekara 20 a matsayin dan wasanta na din din din daga Bayern Munich. (Sky Sports)
Kocin Fulham Marco Silva ne ke kan gaba wajen neman zama sabon kocin Juventus (Sky Italy)











