Arsenal na shirin sayen Sesko, watakila Ronaldo ya koma Al-Hilal

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta fara tattaunawa kan siyan Benjamin Sesko, Manchester United na shirin tayin Kobbie Mainoo koda Bruno Fernandes ya bar kungiyar, Al-Hilal na iya zawarcin Cristiano Ronaldo.
Arsenal ta fara tattaunawa da RB Leipzig a kokarinta na sayen dan wasan gaban kasar Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, wanda ake neman sama da Yuro miliyan 80 (£67.4m) a kansa. (Sky Germany)
Har yanzu kofar Manchester United a bude take don karbar tayi kan dan wasan Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, koda kuwa dan wasan tsakiya kuma dan kasar Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 30, ya bar Old Trafford. (I Paper)
Ana kuma sa ran kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya za ta nada kocin Inter Milan Simone Inzaghi a matsayin sabon kocinta bayan wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Asabar. (Sky Sports)
Al-Hilal sun tattauna kan sayen dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 40, wanda zai iya zuwa kungiyar a kyauta a wata mai zuwa idan bai kulla sabuwar yarjejeniya da Al-Nassr ba. (Sky Sports)
Sai dai Ronaldo ya cimma yarjejeniyar tsawaita zamansa da Al-Nassr. (Foot Mercato)
Al-Hilal na tattaunawa da AC Milan kan cinikin dan wasan baya na kasar Faransa Theo Hernandez, mai shekara 27, wanda ke kan gaba cikin cikin yan wasan da kungiyoyi ke marari a gasar Saudi Pro League a bazara. (Fabrizio Romano)
Jami'ai daga Real Betis za su gana da takwarorinsu na Manchester United a mako mai zuwa don tattaunawa kan makomar dan wasan Brazil Antony mai shekaru 26 da yiyuwar kungiyar Red aljannu ba za ta sake barin shi a matsayin aro ba. (Marca Espanya)
Dan wasan gaban Faransa, Christopher Nkunku, zai bar Chelsea a bazarar nan, yayin da Tottenham ta yi bincike kan yiwuwar siyan dan wasan mai shekaru 27. (Talksport)
Paris St-Germain ta bi sahun Manchester United da Chelsea wajen zawarcin dan wasan tsakiyar Argentina mai suna Franco Mastantuono, mai shekara 17, daga River Plate. (Sky Sports)
Dan wasan gefe na Jamus Leroy Sane, mai shekara 29, an yi masa tayin inganta kwantaraginsa don ci gaba da zama a Bayern Munich. (Sky Germany)
Manchester United da Aston Villa na zawarcin golan Lille dan kasar Faransa Lucas Chevalier mai shekaru 23. (Caughtoffside)











