Hukumar FBI ta nuna shaidar yi wa shari'a tarnaki a gidan Trump

Asalin hoton, OTHERS
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ta gaya wa wani alkali cewa tana sa ran gano shaidar da ke nuna yin tarnaki ga shari’a a binciken da take yi na gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump a Florida, kamar yadda wasu sabbin takardun kotu da aka fitar suka nuna.
Masu bincike sun ce an adana wasu takardun sirri tare da wasu jaridu da mujallu a gidan shugaban da ke Mar-a-Lago.
Ma’aikatar shari’ar ta ce ta sanya takunkumi a kan takardar izinin binciken domin kare shedu farar hula masu yawa kan batun.
A ranar Juma’a 28 ga watan Agusta ne Ma’aikatar shari’a ta Amurkar ta saki irin takardar izinin biciken da hukumar FBI ta yi amfani da ita wajen yin kutse a gidan tsohon shugaban kasar ta gudanar da bincike ranar 8 ga watan nan na Agusta, amma kuma na takaita abubuwan da ke cikin takardar sosai.
Jami’in hukumar binciken ta FBI wanda ya rubuta takardar, ya bayyana cewa suna ganin akwai alamun su yarda cewa akwai shedar wasu abubuwa da suka saba doka da za su gano.
Jami’in ya kuma kara da cewa akwai kuma alamar da kila za ta tabbatar musu da cewa an yi wa doka tarnaki a gidan.
Takardar ta nuna cewa wannan bincike da ake yi wanda ba a taba yin irinsa ba a kan wani tsohon shugaban kasar an fara shi ne bayan da aka gano wasu muhimman takardun bayanan sirri na fadar gwamnatin Amurkar.
An gano su ne daga cikin wasu akwatuna 15 da aka gano a gidan Trump din na Mar-a-Lago a watan Janairu na wannan shekara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A binciken da hukumar ta FBI ta yi kan wadannan takardu na sirri ta bankado wasu takardun sirri 184, wadanda suka hada da wasu 25 da aka ware su a matsayin wadanda suke kunshe da manya-manyan sirri.
Wasu daga cikin wadannan takardu da aka hada su da tsoffin jaridu da mujallu na dauke da rubutun shi Trump.
Tsohon shugaban na Amurka ya dai musanta aikata wani abu ba daidai ba.
Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurkar, Karine Jean-Pierre, ta ce gwamnatin Shugaba Biden ba za ta ce komai ba a game da binciken.
Ta ce, ''kamar yadda abin yake da alaka, kuma yadda na fahimci dalilin da ya sa mutane ke da sha’awa a kan lamarin, mun san haka sosai.
Amma dangane da duk wasu kalamai a kan duk wani abu da ke da dangantaka da wannan bincike mai zaman kansa, hatta a kan wasu abubuwa na musamman, muna ganin bai dace ba mu yi magana a kan wannan.''
Shi dai Mista Trump ya mayar da kakkausan martani kan batun a shafinsa na intanet , Truth Social, yana cewa ‘yan barandan siyasa ne da ‘yan daba ke jagorantar binciken.
Ya ce bai kamata Mai shari’a Bruce Reinhart, wanda ya sa hannu kan takardar izinin gudanar da bincike a gidan nasa ba ya bayar da damar kutse a gidansa ba.
Mista Trump ya zargi alkalin da nuna masa kiyayya. Tsohon shugaban ya ce daman shi tuni ya bayar da umarnin ayyana takardun gaba daya a matsayin na sirri.
Ana sa ran Ma’aikatar shari’ar za ta ci gaba da gudanar da bincikenta a sirri, yayin da take ci gaba da nazartar takardun tare da sa ran za ta gayyato karin shedu.











