Champions League: Real Madrid za ta kara da Atletico, Liverpool da PSG

Champions league

Asalin hoton, EPA

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Jadawalin zagaye na biyu wato last 16 na gasar zakaurn turai ya fito, inda aka rarraba ƙungiyoyin da za su fafata da juna domin tsallakawa zuwa wasan kwata final a gasar ta bana.

Daga manyan wasannin da za su ja hankalin masu kallo, akwai wasan da za a fafata tsakanin Real Madrid ta Spain da Atletico Madrid ita ma ta Spain, da kuma wanda PSG ta Faransa za ta fafata da ƙungiyar Liverpool ta Ingila.

A sauran wasannin, ƙungiyar Barcelona za ta fafata da Benfica, Bayern Munich da Bayer Leverkusen, Club Brugge da Aston Villa, Borussia Dortmund da Lille, PSV Eindhoven da Arsenal sai kuma Feyenoord da za ta doka wasa da Inter Milan.

Haka kuma an shirya jadawanin wasannin na gaba wato kwata final, inda ƙungiyar da ta samu nasara tsakanin PSG da Liverpool za ta fafata ne da wadda ta samu nasara a wasan Club Brugge da Aston Villa.

Haka kuma ƙungiyar da ta samu nasara a wasan PSV da Arsenal ce za ta fafata da ƙungiyar da ta yi nasara a wasan Real Madrid da Atletico Madrid.

Ƙungiyar da ta samu nasara tsakanin Benfica da Barcelona za ta doka wasa da wadda ta yi nasara a wasan Borussia Dortmund da Lille.

A wasannin kusa da na ƙarshe kuwa, ƙungiyar da ta fito a wasannin da za buga tsakanin wadda ta yi nasara a wasan Barcelona da Benfica da na Borussia Dortmund da Lille ce za ta fafata da wadda ta fito a wasan da za a buga tsakanin wadda ta yi nasara tsakanin Bayern Munich da Bayer Leverkusen da na Feyenoord na Inter Milan.

A ɗayan wasan na kusa da na ƙarshen, ƙungiyar da ta fito a wasan tsakanin da aka buga tsakanin wadda ta yi nasara a wasan PSV da Arsenal da wadda ta yi nasara a wasan Real Madrid da Atletico Madrid ce za ta fafata wadda ta fito a wasan da za a buga tsakanin wadda ta samu nasara a wasan PSG da Liverpool da na da Club Brugge da Aston Villa.