ACF ta fasa kafa majalisar magabata a jihar Kano

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, facebook/Abba Kabir Yusuf

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya (ACF), reshen jihar Kano ta sanar da janye matakin da ta ɗauka na shirin kafa wata ƙungiyar magabata a jihar.

ACF ta janye aniyar tata ne sakamakon jan hankalin da gwamnatin jihar ta yi mata ne cewa, tuntuni jihar ta samar da irin wannan majalisa, don haka kafa makamanciyar ƙungiyar bai kamata ba.

A wata sanarwa da ta fitar gwamnatin Kanon ta ce tun a watan Janairun 2024 gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya kafa irin wannan ƙungiya ta dattawa.

Majalisar za ta ƙunshi tsofaffin gwamnnonin jihar da 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa masu ra'ayi daban-daban domin kawar da rarrabuwar kai da tattara shawarwari domin cigaban al'ummar jihar.

Haka kuma gwamnatin ta yi kira ga dukkanin ƙungiyoyi da sauran al'umma da su haɗa kai da tsarin da aka kafa maimakon ƙirƙiro wani makamancinsa sabo.

Shugaban ƙungiyar ta Tuntuɓa ta Arewa, reshen jihar ta Kano, Dakta faruk Umar, wanda suka kafa sabuwar majalisar ya ce da wannan jankali na gwamnatin sun janye nasu tsarin sun kuma yi maraba da matakin gwamnatin jihar na ankarar da su a kai:

''Na yi murna kuma wannan ya nuna mana cewa gwamnati tana lura da abubuwan da mutane ke yi.

''Daman mu abin da muka kalla shi ne muna bukatar haɗin kan dukkanin manyanmu na jihar Kano,'' kamar yadda ya bayya.

''Na biyu kuma mun ga harkar shaye-shaye ta yi yawa wadda ta janyo abubuwa da yawa kamar ƙwacen waya da far wa mutane gida don neman kuɗin fansa, saboda yaran nan in sun sha maye yana zama matsala,'' in ji shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Umar ya ce waɗannan na daga cikin abubuwan da suka kalla suka ga ya dace su kafa irin wannan kwamiti na manya su rubuta wa gwamnati su ba ta shawara.

''Saboda haka mun yi murna da yadda gwamnati ta yaba mana da abin da muka yi sannan ta ja hankalinmu cewa akwai irin wannan kwamiti na gwamnati,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ƙara da cewa, '' kuma a gaskiya idan gwamna zai shugabanci wannan kowa zai fi shiga saboda gwamna ya haɗa kowa da kowa.''

Shugaban ya bayar da tabbacin cewa a yanzu za su janye nasu ƙudurin:

''Za mu janye namu kuma duk waɗanda suka zo mana za mu rubuta wa gwamnati da sunayensu kuma mu roƙi gwamnati wanda ta ga ya kamata su sa shi a cikin na gwamnatin,'' in ji shi.

Dangane da jinkirin da aka samu wajen ƙaddamar da majalisar, wadda gwamnati ta jagoranci kafawa, kwamishinan yaɗa labarai na jihar ta kano Ibrahim Wayya ya ce sha'ani ne irin na shugabanci saboda ana son a sama wa majalisar gindin zama yadda zamanta zai samu duk wata kariya a hukumance da ya kamata ta samu, wanda zai ba ta dama ta iya gudanar da al'amuranta yadda ya kamata.

Kwamishinan ya ƙara da cewa su ma masu ra'ayin kafa wannan sabuwar majalisar suna iya haɗuwa da gwamnati a tafi tare.