Newcastle na fatan sayen Phillips, Neves na tattaunawa da Benfica

An wallafa

Newcastle United na da yaƙinin za su daidaita a cinikin ɗan wasan Ingila mai shekara 28, Kalvin Phillips daga Manchester City sai dai tana fuskantar kalubale daga Juventus, Everton da Crystal Palace. (Telegraph - subscription required)

Ya zama wajibi iyalan Glazer su biya Sir Jim Ratcliffe kusan dala miliyan 66 idan suka rusa yarjejeniyar da aka cimma da kamfaninsa Ineos, da ya saye kashi 25 cikin 100 na Manchester United. (Independent)

A wani ɓangare na yarjejeniyar, dole a tuntube Ineos kan kowanne irin sauyi ko yarjeniyoyin da Manchester United za ta kulla a watan Janairu, kuma babu damar korar kocin kungiyar Erik ten Hag, sai da izinin Ratcliffe. (Standard)

Ratcliffe ya bijiro da wasu tsare-tsare na shekaru takwas da yake ganin za su taimaka wajen inganta United. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya a Portugal Joao Neves, mai shekara 19, da ake alakantawa da Manchester United, na tattaunawa kan sabon kwantiragi da Benfica. Yarjejeniyar ta kunshi ba shi damar tafiya wani kulob din daga kan yuro miliyan 120. (O Jogo - in Portuguese)

Ana alakanta United da kokarin saye ɗan wasan Sweden mai shekara 25 Viktor Gyokeres daga abokiyar hamayyar Benfica wato Sporting Lisbon. (Correio da Manha, via Express)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce kungiyarsa a shirye take wajen ganin ta inganta kulob din a watan Janairu, saboda a yanzu burinsu shi ne ganin sun sake karfi. (Guardian)

Gunners ta kwaɗaitu da ɗan wasan Bayern Munich Matthijs de Ligt sai dai da wuya ɗan wasan mai shekara 24 ya amince da tafiya wata kungiya a cikin watan Janairu. (Athletic - subscription required)

Liverpool ta tambaye Fulham kan yiwuwar iya saye ɗan wasanta asalin Amurka Antonee Robinson mai shekara 26, yayinda suke kokarin ganin an daidaita a cikin watan Janairu. (90 Min)

Tottenham ta fadawa ɗan wasan baya a Ingila Eric Dier da mai buga tsakiya a Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, da kuma mai tsaron raga daga Faransa Hugo Lloris, mai shekara 37, cewa suna iya barin ƙungiyar a kasuwar cinikin 'yan wasa ta Janairu. (Football Insider)

Ɗan wasan gaba a Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 32, ya ce Atletico Madrid ce za ta kasance ƙungiyar da zai taka ledar karshe a Turai, domin burinsa shi ne ya yi ritaya a Amurka. (AS - in Spanish)

AC Milan ta shirya dawo da ɗan wasanta na Italiya mai shekara 24 Matteo Gabbia da ke zaman aro a Villarreal cikin mako na gaba. (Fabrizio Romano)

Roma na kokarin ganin ta cimma yarjejeniya da tsohon ɗan wasan baya a Juventus Leonardo Bonucci. (Gazzetta dello Sport, via Football Italia)