Man City na cinikin Echeverri, Osimhen zai ci gaba da zama a Napoli

An wallafa

Manchester City ta yi nisa a tattaunawa da ɗan wasan River Plate mai shekara 17 Claudio Echeverri, yayinda ita kuma Chelsea ke nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan na Argentina. (Fabrizio Romano)

Barcelona na fuskantar kalubale daga Manchester City kan cinikin ɗan wasan Fluminense na tsakiya Andre, mai shekara 22, yayinda Pep Guardiola da ke farautar matashin daga Brazil, ake ganin yana fuskantar barazana daga Liverpool da Fulham. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Kungiyoyi firimiya na cikin barazana ƙwace musu manyan 'yan wasa daga Saudiyya, inda ake samun karin kulob din Saudiyya da ke nuna zawarcinsu kan manyan 'yan wasan da ke tashe. (Daily Telegraph - subscription required)

Manchester United ta bi sahun Manchester City da Liverpool a zawarcin ɗan wasan tsakiya a Jamus Joshua Kimmich, mai shekara 28 daga Bayern Munich. (Fichajes - in Spanish)

Arsenal ta shirya raba gari da ɗan wasan Ingila mai shekara 24, Eddie Nketiah, kan fam miliyan 40 yayinda take samun tayi daga West Ham da Brentford da Crystal Palace. (Football Insider)

AC Milan za ta cigaba da zama da kocinta Stefano Pioli, duk da cewa ana alakanta tsohon kocin Chelsea da Tottenham Antonio Conte da shirin komawa kungiyar. (Gazetta dello Sport - in Italian)

Manchester United na hangen ɗan wasan tsakiyar Lyon, Rayan Cherki, mai shekara 20, cikin wadanda take fatan saye adaidai lokacin da Erik ten Hag ke nuna matsuwa kan sayen ɗan wasan gaba. (Football Transfers)

Manchester City ta bukaci Barcelona ta biya fam miliyan 26 kan ɗan wasan Portugal mai shekara 29 Joao Cancelo domin ya je zamana aro. (Sport - in Spanish)

Wakilin ɗan wasan gaba a Napoli Victor Osimhen ya yi watsi da raɗe-raɗin da ke nuna matashin ɗan Najeriya zai bar kungiyar a sabuwar kaka duk da sabuwar yarjejenyar fam miliyan 100 da ya ratabawa hannu. (Corriere dello Sport via Football Italia)

Manchester United a shirye take ta amincewa ɗan wasan Ivory Coast Amad Diallo mai shekara 21 ya bar Old Trafford a watan Janairu zuwa Southampton a matsayin aro. (Football Insider)

Paris St-Germain ta amince da biyan fam miliyan 17.5 kan ɗan wasan Sao Paulo mai shekara 20 Lucas Beraldo. Ɗan wasan ya kuma kasance wanda kocin Liverpool Jurgen Klopp ke hari. (L'Equipe - in French)

Tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na shirin karban aikin horas da kungiyar Besiktas ta Turkiyya.(Mirror)

Kocin Al-Ettifaq Steven Gerrard ya bukaci shugabannin kungiyar su aiwatar da sabbin sauye-sauye a watan Janiru domin inganta kuungiyar. (Mail)

Kocin Newcastle Eddie Howe zai tattauna da daraktan wasanni Dan Ashworth kan sabbin cinikin da suke shirin aiwatarwa a watan Janairu. (Newcastle Chronicle)