Arsenal na neman Toney da Pablo, Mbappe ya sauya shawara a kan PSG

An wallafa

Arsenal ta tuntuɓi wakilan Ivan Toney a shirin da take yi na cinikin ɗan wasan na gaba na Brentford kuma ɗan Ingila. (Rudy Galetti)

Haka kuma Arsenal ɗin ta sanya sunan matashin ɗan wasan tsakiya na Sao Paulo Pablo Maia ɗan Brazil mai shekara 21 a cikin jerin waɗanda za ta nema a watan Janairu. (Football Transfers)

Kylian Mbappe ba ya son barin Paris St-Germain a watan Janairu duk da cewa kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar nan. (L'Equipe)

Fulham za ta nemi kuɗin da ya kai fam miliyan 60 a watan Janairu daga duk wata ƙungiya da ke son ɗan wasanta na tsakiya na Portugal Joao Palhinha, wanda ake alakantawa da tafiya Bayern Munich, ko Liverpool ko kuma Arsenal. (Football Insider)

PSG ta ƙulla yarjejeniya ta baka domin sayen ɗan wasan baya na Sao Paulo Lucas Beraldo, wanda Liverpool ke hari. Ɗan Brazil din mai shekara 20 zai bar ƙungiyar tasa a wata mai kamawa na Janairu a kan fam miliyan 17. (Fabrizio Romano daga Goal)

Inter Milan na da ƙwarin gwiwa za ta yi nasara a kan Manchester City a zawarcin ɗan wasan gaba na ƙungiyar Club Bruges, Tajon Buchanan na Kanada. (Gazzetta dello Sport)

Strasbourg na duba yuwuwar sayen matashin ɗan bayan Boca Juniors, Valentin Barco, ɗan Argentina mai shekara 19, wanda Chelsea ma na sonsa, a watan Janairu. (Evening Standard)

Ita ma ƙungiyar Brighton ta bayyana sha'awarta a kan Barco har ma ta gana da wakilansa. (TYC Sports)

Tottenham na sa ido a kan Radu Dragusin bayan da ta tura masu farauto mata ƴan wasa suka kalli matashin ɗan Romania, mai shekara 21 a karawar Genoa da Juventus a makon da ya gabata. (Fabrizio Romano)

Lyon na harin sayen ɗan wasan gaba na gefe na West Ham, Said Benrahma na Algeria, a watan Janairu. (Talksport)

Aston Villa ta bi sahun Tottenham a zawarcin ɗan wasan gaba na gefe na Juventus Samuel Iling-Junior, mai shekara 20, da tayin kusan fam miliyan 17 da ake ganin za su iya isa cinikin ɗan tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21.(Football Insider)

Barcelona na sha'awar ci gaba da riƙe ɗan gaban Atletico Madrid Joao Felix, da ta ara, har zuwa bayan kakar nan, amma kuma za ta sake ƙulla yarjejeniyar aron ne saboda ba za ta iya sayen ɗan Portugal ɗin ba gaba ɗaya. (Goal)

West Ham ta bi jerin masu zawarcin ɗan bayan Bayer Leverkusen Jonathan Tah na Jamus, wanda ya fi son tafiya gasar Premier a kan Bayern Munich. (Bild daga Fussball Transfers)

Lille na nazarin sayen ɗan gaban Southampton Sekou Mara da ke tawagar Faransa ta ƴan ƙasa da shekara 21, a watan Janairu. (L'Equipe)

Ɗan bayan Barcelona Ronald Araujo, ɗan Uruguay mai shekara 24 yana son ci gaba da zama da zakarun na La Liga duk da sha'awarsa da Bayern Munich ke yi. (Sky Sports)

Tottenham da Monaco na son ɗaukan Tosin Adarabioyo, idan kwantinragin ɗan bayan mai shekara 26 ya ƙare da Fulham a ƙarshen kakar nan. (90min)

Newcastle za ta kawo ƙarshen zaman aron da ɗan wasantsa na tsakiya Joe White ke yi a Crewe domin matashin mai shekara 21 ya tafi Stockport County aro har zuwa ƙarshen kakar nan. (Football Insider)