Waiwaye: Zargin Amnesty kan sojojin Najeriya da dambarwar ƙudirin haraji

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Fararen hula 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin Najeriya - Amnesty

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

A cikin wannan makon ne ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi zargin cewa fararen hula kusan 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin Najeriya, tun bayan fara yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas.

Shugaban ƙungiyar ta Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Maiduguri, ya kuma zargi Boko Haram da sojoji da laifukan take ƴancin ɗan'adam.

A cewarsa, dakarun soji sun take ƴancin bil'adama yayin gudanar da ayyukansu a yankin na arewa maso gabas.

To sai dai shalkwatar tsaron Najeriyar ta musanta duka zarge-zargen na Amnesty cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.

Majalisar dattawa ta kafa kwamati don sake nazarin dokar haraji

Shugaban majalisa

Asalin hoton, Nigerian Senate

A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da jingine aiki kan ƙudirin dokokin haraji da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin - wanda ya jagoranci zaman - ne ya sanar da hakan yayin da suke muhawara zauren majalisar.

Barau ya kuma sanar da kafa wani kwamati da zai yi aikin dubawa da kuma gyara saɗarorin dokar da ke jawo taƙaddama, musamman daga yankin arewacin ƙasar.

To sai dai a ranar Alhamis Shugaban majalisar Dattawan Sanata, Sanata Godswill Akpabio za ta ci gaba da tattauna batun ƙudurorin haraji, domin ba ta dakatar da su ba.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar ya bai wa ministan shari'ar ƙasar umarnin zama tare da majalisar domin tattauna batutuwan da suka janyo taƙaddama a ƙudirin.

An jibge jami'an tsaro a fadar masarautar Kano

Fadar Sarkin Kano Sanusi II
Bayanan hoto, Fadar Kano da ke Ƙofar Kudu ita ce gidan sarkin Kano a hukumance.

A safiyar Juma'a ne kuma jami'an tsaro suka yi wa fadar sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu ƙawanya.

Hakan ya kawo cikas ga zirga-zirga da shige da fice a cikin fadar mai ɗimbin tarihi, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke da zama.

Ana iya ganin jami'an tsaro da kuma motocin tarwatsa masu zanga-zanga waɗanda aka jibge a fadar.

Bayanai sun nuna cewa dama an tsara ranar Juma'a Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi wa ɗaya daga cikin masu riƙe da sarauta mafi girma a masarautar, Wamban Kano, Mannir Sanusi rakiya zuwa Bichi domin kama aiki a matsayin hakimi.

An yanke wa ma'aurata hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jigawa

hukunci

Asalin hoton, Getty Images

A tsakiyar makon da muke bankwanar da shi ɗin ne kuma wata babbar kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wasu ma'aurata hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe wata mata mai suna Salamatu.

Kotun ta ce ta same su da laifin kashe matar mai kimanin shekara 30, wadda suka zarga da mutuwar ɗansu sanadiyyar maita.

Da yake yanke hukunci, mai sharia'a Ado Yusuf Birnin-Kudu, ya ce kotun ta same su da laifin aikata kisan, don haka ne ta yanke musu wannan hukunci.

Mun kashe ƴan ta'adda dubu takwas a Najeriya cikin 2024 - Sojoji

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan ta'dda 8,034 daga farko zuwa ƙarshen shekara ta 2024.

Wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar, ta ce an samu nasarar ne a samame daban-daban da sojoji suka kai yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da arewa maso tsakiya da kuma sauran yankunan ƙasar.

Ya ce an kama wasu 'ƴan ta'dda' 11,263 da kuma ceto mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su.

"Mun kuma samu nasarar ƙwato makamai 8,216 da harsasai 211,459. Mun kuma daƙile yunkurin satar ɗanyen mai da kuɗinsa ya kai sama da naira biliyan 57," in ji Buba.

EFCC ta ƙwace unguwa guda daga wani tsohon jami'in gwamnati a Abuja

Anguwa guda da EFCC ta ƙwace

Asalin hoton, EFCC/X

Hukumar EFCC ta samu nasarar ƙwace kadara mafi girma a tarihinta, inda a ranar Litinin, 2 ga watan Disamban 2024, mai shari'a Jude Onwuegbuzie ya mallaka wa gwamnati wani rukunin gidaje, wanda aka gina a fili mai mai faɗin murabba'in ƙasa 150,500, mai ɗauke da rukunin gidaje 753 da wasu gine-ginen a Abuja.

Wannan shi ne ƙwace kadara mafi girma tun bayan kafa hukumar EFCC a shekarar 2003.

Kotu ta ƙwace rukunin gidajen ne mai lamba 109 a yankin Zone C09 da ke unguwar Lokogoma a Abuja, wanda kotun ta ce ta mallakin wani tsohon jami'in gwamnati ne, kamar yadda wata sanarwa da EFCC ta fitar ta nuna.

Mutum shida sun mutu, takwas sun ji rauni bayan motarsu ta taka bam a Zamfara

Mota ta taka bam

Asalin hoton, Channels TV

Aƙalla mutum shida ne suka mutu wasu takwas kuma suka ji munanan raunuka bayan da wata motar fasinja ta taka nakiya da ake zargin 'yan bindiga ne suka dasa ta, a kan hanyar zuwa garin Ɗansadau da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Al'ummar garin na Ɗansadau sun tabbatar wa BBC da afkuwar lamarin, inda suka ce motar fasinjar ƙirar Golf, na tafiya ne lokacin da ta taka wannan nakiyar, wadda kuma ta yi fata-fata da motar.

Mazauna yankin sun ce a yanzu, suna cikin fargabar fuskantar wannan sabon salon kai hari da 'yan bindigar ke amfani da shi, domin hana jami'an tsaro kai musu hari da kuma ke zama wani matakin kashe jama'a musamman matafiya.

Duk wani ƙoƙari da BBC ta yi na ji daga ɓangaren gwamnatin Zamfara, kan al'amarin ya ci tura, yayin da ita ma rundunar 'yansandan jihar kiran wayar da BBC ta yi don jin ta bakinta ba ya shiga.

Gwamnatin Jigawa ta karrama gwarzuwar Hikayata ta BBC Hausa

Gwarzuwar Hikayata ta BBC Hausa
Bayanan hoto, Gwarzuwar Hikayata ta BBC Hausa

Gwamnatin jihar Jigawa, ta karrama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024, Hajara Ahmed Hussain.

A wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Dutse, Gwamnan jihar Malam Umar Namadi, ya bai wa gwarzuwar kyautar kuɗi naira miliyan biyu da kuma ɗaukar nauyin karatunta na digiri.

An yi bikin karramawar ne a gaban kwamishinoni da iyaye da kuma ƴaƴanta biyar.

A ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata Hajara Ahmed Hussaini ta zama gwarzuwar gasar gajerun ƙagaggun labarai da BBC Hausa ke shiryawa, wato Hikayata da labarinta mai take 'Amon 'Yanci'.