Real Madrid na neman ƴan wasan Premier, Utd na son Adeyemi

Rodri na ɗaya daga cikin ƴan wasan da Real ke nema daga Premier

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid na harin sayen ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri, na Sifaniya da ɗan bayan Liverpool Trent Alexander-Arnold da kuma ko dai ɗan bayan Arsenal's William Saliba na Faransa ko kuma ɗan bayan Tottenham Cristian Romero, na Argentina. (Independent)

To amma kuma Tottenham na shirin gabatar wa Romero sabon kwantiragi domin hana wasu ƙungiyoyin jan hankalinsa. (Football Insider)

Manchester United na sha'awar ɗan gaban Borussia Dortmund Karim Adeyemi na Jamus mai shekara 22, amma kuma za ta iya fuskantar gogayya daga Newcastle da Liverpool. (Teamtalk)

Newcastle na daga cikin ƙungiyoyin Premier da suke son ɗan wasan tsakiya na Lille Angel Gomes na Ingila, wanda kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kaka. (Football Insider)

West Ham da Manchester United na matuƙar son ɗan wasan tsakiya na Jamus Leon Goretzka, wanda ba ya cikin farin ciki ganin yadda ya rasa matsayinsa a Bayern Munich. (Sun).

Everton na ɗaukar mai tsaron ragar Ingila Jordan Pickford a matsayin ɗaya daga cikin muhimman 'yan wasanta saboda haka ba ta da wani shiri na maye gurbinsa da Nick Pope na Newcastle, shi ma na tawagar Ingila. (Teamtalk)

Ɗn gaban Faransa Anthony Martial, na dab da kammala tafiya AEK Athens, a matsayin wanda ba shi da ƙungiya tun bayan da ya bar Manchester United da bazara. (Fabrizio Romano)

Wataƙila Arsenal da Newcastle su je neman Leroy Sane, na Jamus, wanda aka ce ba ya jin daɗin zamansa a Bayern Munich. (Caught Offside)

Aston Villa, da Nottingham Forest, da Wolves da kuma West Ham na daga cikin ƙungiyoyin da suke son ɗan bayan Red Bull Salzburg Oumar Solet na Faransa. (HITC)

Liverpool na son samo ɗan wasan tsakiya mai tsaro da kuma babban ɗan baya na ɓangaren hagu a watan Janairu. (Football Insider)

Arsenal na sa ido a kan ɗan gaban Kanada Jonathan David, mai shekara 24, wanda ke shiga shekararsa ta ƙarshe ta kwantiraginsa a Lille. (Caught Offside)

Bournemouth, da Fulham da Wolves na sha'awar ɗan bayan Kamaru Joel Matip, mai shekara 33, wanda har yanzu ba shi da ƙungiya bayan ya bar Liverpool a bazara (HITC)