Real Madrid ta fara Champions League na bana da kafar dama

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta fara Champions League na bana da kafar dama, bayan da ta doke Stuttgard 3-1 ranar Talata a Santiago Bernabeu.
Mai rike da kofin bara na 15 jimilla, ta fara cin ƙwallo ta hannun Kylian Mbappe daga baya Stuttgard ta farke ta hannun Jamie Leweling.
Daf da za a tashi daga karawar Antonio Rudiger ya ci na biyu, sannan Endrick ya zura na uku a raga, hakan ya bai wa Real Madrid maki ukun da take bukata.
Wannan shi ne karon farko da Real Madrid ta kece raini da Stuttgard a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai.
Kawo yanzu Real Madrid ta yi wasa 14 a gida a jere ba tare da an doke ta ba a Champions League, wadda da ta yi nasara 11 da canjaras uku.
Stuttgard ta yi fatan yin wani abu a Bernabeu, bayan da ta san cewar Real Madrid ta yi waje da Bayern a daf da karshe da doke Dortmund a wasan karshe a bara.
Da wannan sakamkon Real Madrid za ta buga wasa na biyu a Champions League a gidan Lille ranar Laraba 2 ga watan Oktoban 2024
Kafin nan Real Madrid za ta karɓi bakuncin Espanyol a wasan mako na shida a La Liga ranar Asabar 21 ga watan Satumba.
Ƴan Real Madrid da suka fuskanci Stuttgard:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni da kuma Arda Güler.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo da kuma Endrick.











