Ƴan wasa na daf da yin yajin aiki - Rodri

Rodri

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester City, Rodri ya ce ƴan wasan tamaula na daf da yin yajin aiki, sakamakon da aka kara yawan wasannin da za suke bugawa.

City za ta kara da Inter Milan ranar Laraba a Champions League, wanda aka kara wasa biyu kafin karawar zagaye na biyu a sabon fasalin babbar gasar zakarun Turai ta bana.

A gasar Club World Cup kuwa, inda City za ta fafata daga baɗi, an kara ƙungiyoyi sun kai 32, an samu karin wasanni da yawa kenan.

''Ina jin muna daf da yin yajin aiki,'' in ji Rodri lokacin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida.

''Idan har an ci gaba da haka, za a kai lokacin da ba mu da wani zaɓi, amma mu ɗan kara jira mu gani.''

A sabon fasalin Champions League da Club World Cup na nufin City za ta buga karin wasa huɗu a kakar daga bana bana, fiye da yawan da ta kara a bara.

Wasa biyu kacal City ta yi ta kuma lashe Club World Cup a Disamba, amma a kakar baɗi za ta yi karawa uku a cikin rukuni da huɗu a zagayen gaba har kai wa karawar karshe.

A kaka biyu baya, City ta buga wasa 120 a dukkan karawa, yayin da Rodri ya buga wasa 63 a kwana 343 a 2023-24

Rodri, wanda ya buga wa tawagar Sifaniya da City wasa 63 a bara, ya lashe Premier League da kofin nahiyar Turai da ya buga cikin wata biyu.

Bayan tashi daga Champions League karawar daf da karshe a gidan Real Madrid, Rodri ya sanar a cikin watan Afirilu cewar yana bukatar hutu.

Bai buga wa City wasa uku da fara kakar bana ba, ya fara daga 2-1 da ta doke Brentford a Premier League ranar Asabar, kwana shida tsakani da ya yiwa Sifaniya Nations League.

Bayan kammala kakar 2023/224 - wadda aka fara daga 6 ga watan Agustan 2023 da aka kammala a kwana 343, ranar 14 ga watan Yuli Rodri ya sanar cewar yana bukatar dogon hutu fiye da wanda ake bashi.