Waiwaye: Kalaman ɓatanci tsakanin Atiku da Tinubu, kuɗaɗen waje 'na sata' da gwamnatin Buhari ta ƙwato
A wannan maƙala, mun duba wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi.
Gwamnatin Buhari ta ƙwato kuɗaɗen waje miliyan 12 'da ma'aikatan gwamnati suka sace'

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi nasarar ƙwato dukiyar ƙasar da wasu jami'an gwamnati suka sace a kuɗaɗen ƙasar waje da suka ƙunshi fan miliyan 6.3 da yuro miliyan 5.4 da dala 390,000.
Ministan Shari'a Abubakar Malami ya ce ana amfani da wasu daga cikin kuɗaɗen wajen aiwatar da wasu ayyuka kamar ginin hanyar Abuja zuwa Kano, da Legas zuwa Ibadan, da kuma ginin gadar Second Niger Bridge a yankin kudu maso gabas.
Ministan ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron bayyana ayyukan gwamnatinsu ta APC tun daga 2015 zuwa yanzu.
Kazalika, ya ce gwamnatin ta Muhammadu Buhari ta samu naira biiliyan 1.8 a cikin gida sakamakon sayar da kadarorin da aka ƙwace daga hannun wasu mutane daga 2015 zuwa 2022.
Ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen 2023 ba - Inec

Asalin hoton, Inec
Shugaban Hukumar Zaɓe a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya jaddada shirinsu na gudanar da babban zaɓe na 2023 a lokacin da aka tsara, yana mai cewa "ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen ba".
Ya ba da tabbacin ne yayin da ya gana da jam'iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen, inda ya gabatar musu da kundin rajistar masu kaɗa ƙuri'a da yawansu ya kai miliyan 93.4.
"Babban zaɓen 2023 zai gudana yadda muka tsara shi. Duk wani rahoton da ya ruwaito saɓanin haka ba matsayarmu ba ce," kamar yadda ya jaddada.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (Inec) ta tsara gudanar da zaɓen daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za a zaɓi shugaban ƙasa da 'yan majalisar tarayya, daga baya kuma a zaɓi gwamnoni da 'yan majalisar jiha a watan Maris.
Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami'in Inec ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro za su sa a ɗaga zaɓen a wasu yankunan Najeriya.
"Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin zaɓen ballantana ma ɗage shi. Irin tabbacin da jami'an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma'aikatanmu ya ƙarfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu," in ji farfesan a ranar Laraba.
Inec ta tsawaita wa'adin karɓar katin zaɓe

Asalin hoton, Inec
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar zaɓe a Najeriya (Inec) ta tsawaita wa'adin karɓar katin zaɓe da take rabawa a faɗin ƙasar da kwana takwas.
Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Inec Festus Okoye ya ce an ɗauki matakin ne don bai wa masu kaɗa ƙuri'a isasshen lokaci na karɓar katin kafin fara jefa ƙuri'a a babban zaɓe na 2023.
"Saboda wannan dalilin, an tsawaita wa'adin karɓar katin zaɓen da kwana takwas," in ji shi. "A madadin wa'adin ya ƙare ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu, za a ci gaba da karɓa har zuwa Lahadi, 29 ga wata."
Inec ta ce lokacin karɓar katin shi ne 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a kowace rana - har Asabar da Lahadi.
Kazalika, tsawaitawar ta shafi dukkan matakan raba katin na ƙaramar hukumar da kuma mazaɓa.
A ranar 25 ga watan Fabarairu ne za a fara kaɗa ƙuri'a, inda ake sa ran 'yan Najeriya miliyan 93.4 da ke da rajistar zaɓen za su zaɓi shugaban ƙasa da 'yan majalisar tarayya. Sai kuma gwamnoni da 'yan majalisar jiha da za a zaɓa a watan Maris.
Yadda PDP da APC ke jifan Tinubu da Atiku da kalaman ɓatanci

Asalin hoton, PPD/APC
'Yan takarar shugaban ƙasa na manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya na jefa wa junansu zarge-zarge game da lafiyarsu da kuma cin hanci da rashawa yayin da ya rage saura kwana 43 a gudanar da babban zaɓen ƙasar na 2023.
Tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ce ta fara sukar Atiku Abubakar, na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, tana mai cewa ba shi da lafiyar jagorantar Najeriya.
Tinubu ya ce ya kamata 'yan Najeriya su ji da lafiyar Atiku domin su yana da cikakkiyar lafiyar gudanar da mulki.
Da suke mayar da martani, tawagar kamfe ɗin Atiku ta zargi Tinubu da aikata cin hanci da rashawa, tana mai cewa "Tinubu kansa shi ne cin hanci".
Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne daga 1999 zuwa 2007, yana da shekara 76 da haihuwa. Shi kuwa Tinubu, wanda tsohon gwamna ne a Jihar Legas tsawon shekara takwas daga 1999 zuwa 2007, shekararsa 70 da haihuwa.
An daɗe ana tafka muhawara kan ƙoshin lafiyar 'yan takarar shugabancin ƙasa a Najeriya, inda Shugaba Buhari da ke mulki a yanzu ya shafe watanni yana jinya a Birtaniya a wa'adin mulkinsa na farko.
Tuni 'yan takarar suka fara karaɗe lungu da saƙo don yaƙin neman zaɓe, inda Tunubu ya ziyarci Jihar Enugu a ranar Laraba, shi kuma Atiku ya tafi Birtaniya duka don neman ƙuri'a a gida da wajen ƙasa.
Ga cikakken labarin a nan:
'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma a Osun
'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoma biyu a yankin Ileogbo da ke jihar Osun.
Jaridar Premium Times a Najeriya ta ce an sace manoman a ranar Laraba lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.
Wata majiyar tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce manoman na tafiya ne tare da wasu mutane bakwai a lokacin da masu garkuwan suka far wa motar su a unguwar Oke Osun da ke Ileogbo.
Majiyar ta ci gaba da cewa sauran bakwai da aka kashe sun tsere amma masu garkuwan sun tafi da manoman biyu.
Wata majiya mai tushe wacce kuma ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro ta ce masu garkuwan sun tuntuɓi iyalan wadanda aka kashe a ranar Alhamis inda suka bukaci a biya su fansar naira miliyan 10.
Kwamandan jami'an tsaro na Amotekun a jihar Osun, Amitolu Shittu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Zan tattauna da masu tayar da ƙayar baya idan na zama shugaban ƙasa - Peter Obi

Asalin hoton, Channels TV
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party a Najeriya, Peter Obi, ya ce zai buƙaci ya tattauna da duk wani ɗan gwagwarmaya ko kuma masu tayar da ƙayar baya da gwamnatin Najeriya ta ɗaure idan ya samu mulkin ƙasar.
Mista Obi ya bayyana haka ne a wani zauren tattaunawa da tambayoyi da gidan talabijin na Channels a Najeriya ya shirya ga ɗan takarar da mataimakinsa.
Ko da wani ya tambayi Mista Obi ko cikin waɗanda zai tattauna da su har da ƴan Boko Haram da ke jawo matsaloli a arewacin Najeriya da kuma ƴan ƙungiyar IPOB da ke kudu maso gabashin ƙasar, sai ya ce:
"Zan tattauna da dukkansu, ko ma wace irin bindiga ce suke ɗauke da ita". Obi ya ce ko da mutum yana ɗaure a gidan yari ne zai je ya fito da shi domin su zauna su tattauna.
Mista Obi ya ce ya yanke hukuncin yin haka ne domin ganin cewa an samu zaman lafiya a ƙasar.
"Zan tattauna da waɗanda suke so a tattauna da su. Sai an kalli me ke jawo suke gwagwarmaya; batu ne na rashin adalci ko lamari ne na talauci ko rashin aikin yi," in ji Mista Obi.
Ku karanta cikakken labarin a nan:









