Majalisar wakilan Amurka ta dakatar da dukkan tallafin da ake bai wa Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar wakilan Amurka ta amince da wani ƙuduri wanda zai dakatar da dukkan wani tallafi da Amurka take bai wa Najeriya har sai ƙasar ta ɗauki matakan daƙile matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar.
A baya ƙudurin ya bai wa Amurka damar riƙe kashi 50% ne na tallafin, amma a yanzu majalisar ta ƙara shi zuwa kashi 100%.
Ɗan majalisa Gregory Stuebe mai wakiltar gunduma ta 17 a majalisar wakilan Amurka daga jihar Florida ne ya gabatar da batun a zauren majalisar ranar Laraba.
Ɗan majalisar wanda ya wallafa bidiyon yadda aka tattauna kan ƙudurin a shafinsa na X, ya ce: "An amince da gyaran da na gabatar kan ƙudurin da ke neman Amurka ta daina bai wa Najeriya tallafi har sai gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan hana yanka Kiristoci.
"Bai kamata a riƙa amfani da kuɗin harajin da Amurkawa ke biya wajen taimaka wa gwamnatin da ta kawar da idon ta ba, yayin da ake sacewa da azabtarwa da kuma kashe Kiristoci ba.
"Babu sauran ɓarna da kuɗaɗe a matsayin tallafi ga ƙasashen waje!" in ji shi.

Asalin hoton, Somodevilla/Getty Images
Tun farko majalisar wakilan ƙasar ta buƙaci a riƙe rabin tallafin da aka ware wa Najeriya ne a watan Afrilu, har sai lokacin da sakataren harkokin waje na ƙasar ya ce gwamnatin Najeriya ta ɗauki "ƙwararan matakan daƙile rikicin ƙasar da kuma hukunta masu hannu a ciki".
Steube ya ce "riƙe kashi 50% kaɗai na tallafin da aka ware wa Najeriya tamkar jinjina wa gwamnatin Najeriya ne duk da cewa ta gaza sauke babban nauyin da ya rataya a wuyanta na kare al'ummarta".
"Na miƙe domin kare ƙudurina na ƙara yawan kuɗin da za a riƙe, daga kashi 50% zuwa kashi 100%. Haka nan sharuɗɗan da aka shata na tilasta Najeriya ta ɗauki matakan magance rikicin da addabi ƙasar," in ji Steube.
Ya ƙara da cewa: "Najeriya ta fuskanci munanan rikice-rikice waɗanda gurɓatattun shugabanninta suka gaza magancewa.
"A tsawon shekaru, musamman a watannin baya-bayan nan, Kiristoci da tsirarun masu bin wasu addinai na fuskantar muzgunawa da ta'addanci daga hannun masu tsattsauran ra'ayi wadanda ke tafka munanan ayyuka".
Da gaske ne ana kashe Kiristoci a Najeriya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan da ɗan majalisar dokokin ƙasar Amurka, Sanata ted Cruz ya zargi gwamnatin Najeriya da bari ana yi wa Kiristoci "kisan kiyashi", hukumomi da al'ummu da dama sun mayar da martani.
Sanata Ted Cruz dai ya gabatar da ƙudirin ne a gaban majalisar dattawan Amurka a watan Satumban 2025, inda ya yi zarge-zargen.
Gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen na Sanata Ted Cruz, cewa ana harar Kiristoci ne inda ta ce ƙungiyoyn da suke yin hare-haren suna harar ƴan Najeriya ba tare da banbanci ba, sannan ta kuma amince da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar amma ta ce ana samun cigaba.
Gwamnatin ta kuma musanta zargin cewa ba sa yin komai wajen hana kisan Kiristocin.
Ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙari wajen fattakar 'ƙungiyoyin ƴan ta'adda' a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyin ƴanƙasar, kuma ana ganin sakamakon hakan.
''Tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Fabrairun 2025 kadai, fiye da ƴanbindiga 13,543 ne sojojinmu suka kashe tare da kuɓutar da kusan 10,000 da ake garkuwa da su a faɗin ƙasar'', a cewar gwamnatin ƙasar.
A nata ɓangaren majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da zarge-zargen na sanata Ted Cruz ta kuma amince da aike da tawaga zuwa Amurkar domin fahimtar da su yadda batun yake.
Majalisar ta ce zarge-zargen babbar barazana ce ga hadin kan Najeriya.
Ƴan Majalisar sun yanke shawarar yin aiki tare da gwamnatin tarayya kan matakan da suka fi dacewa na yaƙi da ta'addanci da kuma matsalar tsaro.
Yaushe matakin zai fara aiki?
Wajibi ne sai majalisar dattijan Amurka ta amince da ƙudurin, kuma shugaban ƙasa ya sanya hannu a kansa kafin ya fara aiki.
Wannan na nufin amincewa da ƙudurin da majalisar ta yi a ranar Laraba ba zai sauya komai ba tukuna game da tallafin da Amurka ke bai wa Najeriya.
Matakin na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta a shekarar 2025 bisa zargin cin zarafin mabiya addinin Kirista, da kuma harin da Amurka ta ƙaddamar a cikin Najeriya wadda ta ce ta kai ne a kan 'ƴan ta'adda'.
A watannin da suka gabata Najeriya da Amurka suka sanar cewa sun ƙulla wata alaƙar soji domin yaƙi da ayyukan masu kai hare-hare a ƙasar.










