Wace riba Tinubu ke samu daga takarar Muslim-Muslim?

Asalin hoton, Getty Images
A ƙarshen makon da ya gabata ne jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sake zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2027, bayan miƙa sunayensu ga hukumar zaben kasar INEC.
Wannan dai ya kawo ƙarshen fargaba da jita-jita da aka daɗe ana yi dangane da batun mutumin da zai zama mataimakin Tinubun, inda wasu suka yi fargabar sauya mataimakin bisa dalilai guda biyu: na addini da na siyasa.
Addini da bangaranci na taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, musamman abin da ya shafi shugabancin kasa.
Wasu sun yi zaton Tinubu zai iya sauya Kashim Shettima da wani daban daga arewacin ƙasar sakamakon matsin lamba daga wasu jama'u da ƙungiyoyin addini cewa bai kamata shugaba da mataimakinsa su zama masu addini iri ɗaya ba.
"Lallai al'amarin ba zai yi wa wani bangaren al’umma daɗi ba kuma ba za ka zarge su ba kasancewar a Najeriya an fi bai wa addini da ɓangare muhimmanci fiye da cancanta. Shi ya sa ma tun 1999 jam'iyyu ke lura da batun cimma daidaito wajen takara," in ji Farfesa Yahaya Tanko na jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto.
Tambayar da ƴan Najeriya ke yi a yanzu haka ita ce mene ne tasirin irin wannan takara sannan kuma ta yaya zai shafi siyasar ƙasar a nan gaba?
Me ya sa Tinubu ke son takarar Muslim-Muslim?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Kabiru Sufi malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, CAS sannan mai nazarin kimiyyar siyasa, ya ce ba wani abu ba ne ya sa Tinubu rungumar takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa dukka Musulmi illa buƙata.
"Batu ne na buƙata ta samun nasara a arewacin Najeriya kasancewar ɗaukar mabiyin addinin Kirista a matsayin mataimaki a arewacin Najeriya ka iya raunana takarar. Sannan wataƙila an yi hakan ne bisa dogaro da zaɓen da aka rushe na 12 ga watan Yuni wanda ya bai wa MKO Abiola da Babagana Kingibe nasara a faɗin ƙasar."
Dangane kuma da wane dalilin ne ya sa Tinubun bai sauya daga takarar Muslim-Muslim ba sai dakta Sufi ya ƙara da cewa:
"Idan aka duba aka yi nazarin shekarun da aka kwashe ana wannan mulki na Muslim-Muslim ɗin kusan za a iya cewa babu alamu da suka nuna takarar tana da cutarwa ga mabiya addinin Kirista. Akwai masu ganin kamar an fi kyautata musu."
Wane tasiri Muslim-Muslim zai yi a siyasar Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Kabiru Sufi ya ce nasarar ko akasinta da takarar Muslim-Muslim za ta samu a 2027 ne zai bayyana irin tasirin da za ta yi a siyasar ƙasar.
"Nasararta a karo na biyu zai sa tasirin batun shigar da addinin a wajen samar da daidaito zai iya raguwa ta yadda kowane ɗan siyasa ka iya ɗaukar mabiyin kowane addini kuma ba tare da an yi ƙorafi ba tunda an yi ya wuce sannan an ƙara yi ya wuce ba tare da cutarwa ba.
‘’To wataƙila wannan ya sa a yi ƙasa da batun samar da daidaito ta fuskar addini inda za a rage kiraye-kiraye da tayar da jijiyar wuya musamman daga ɓangarorin addinai guda biyu," in ji Dakta Sufi.
Sai dai kuma masanin kimiyyar siyasar ya ce ko da takarar ta samu nasara ba za ta rasa ƙalubale ba.
"Duk da haka wannan ba zai sa ɗari bisa ɗari al'amarin ya samu karɓuwa ba. Akwai ƙalubale a wasu yankunan musamman yankunan da addini ɗin ya yi tasiri."
Illa da ƙalubalen takarar Muslim-Muslim
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma Farfesa Tanko Yahaya na sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto ya ce babban ƙalubale da takarar ta ba-sabun-ba ta fuskanta shi ne irin ƙurar da ta tayar a 2023.
Ya kuma ƙara da cewa ƙurar ta wuce hayaniya da tayar da jijiyar wuya inda ya ce hatta a ƙuri'ar da aka kaɗa da yadda ƙuri'ar ta raba kan ƴan ƙasa ya nuna irin ƙalubalen.
"Akwai mamaki kan yadda shi Peter Obi wanda za a iya cewa sabon shiga ne dangane da abin da ya shafi takarar shugaban ƙasa ya samu ƙuri'u masu yawa da suka sa ya zo na uku...kuma wannan bai rasa nasaba da irin ƙuri'un bore da al'ummar Kirista suka kaɗa wajen zaɓar shi Peter Obi ɗin domin ƙaurace wa zaɓar Tinubu na APC mai takarar Muslim-Muslim," in ji Farfesa Yahaya.
Masanin kimiyyar siyasar ya ƙara da cewa duk da ba wannan ne karon farko na samun Musulmai biyu na takara a matsayin shugaba da mataimakinsa ba amma takarar Muslim-Muslim a 2023 ta tarar da sauyin zamantakewa tsakanin mabiya manyan addininan Najeriya biyu.
"Duk da cewa ba za ka iya kamanta takarar MKO Abiola da Babagana Kingiɓe a 1993 da ta Tinubu da Kashim Shettima a 2023 ba, sakamakon sauyin yanayin zamantakewa. A wancan lokacin akwai fahimtar juna amma yanzu akwai rauni na zamantakewa tsakanin al'ummomi. Kuma hakan ne ya sa ake ganin batun takarar Muslim-Muslim ya tayar da ƙura."
Farfesa Yahaya ya kuma ce za a iya sake samun irin wannan tayar da ƙura saboda ba a la'akari da dacewa ko cancanta illa addini da ɓangaranci.
"Idan dai har aka ci gaba da wannan tikitin to a zaɓen 2027 ma haka za a samu rabuwar kai. Wasu Musulmai suna kare tikitin Muslim-Muslim, haka nan wasu mabiya addinin Kirista suna sukar sa tare da karkatar da ƙuri'unsu ga ɗan takarar da ya dace da addininsu," in ji Farfesa.
Lokuta huɗu na takarar Muslim-Muslim a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- 1993:
Takarar MKO Abiola da Babagana Kingibe a zaɓen shugaban ƙasa na 1993. MKO Abiola Musulmi ne daga Kudu maso Yamma, sannan Babagana Kingibe ma Musulmi ne daga Arewa maso Gabas. Sun yi takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa a ƙarƙashin jam'iyyar SDP.
- 2019
Takarar Nasiru El-Rufai da Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin gwamna da mataimakiyarsa. El Rufai Musulmi ne daga Kaduna ta tsakiya, ita kuma Hadiza ta kasance Musulma ce daga Kudancin Kaduna inda mafi rinjaye mabiya addinin Kirista ne.
- 2023
Gwamna Uba Sani da Hadiza Sabuwa Balarabe a 2023: Gwamna Uba Sani wanda Musulmi ne daga Kaduna ta tsakiya ya ɗauki Hadiza Sabuwa wadda Musulma ce daga kudancin Kaduna.
- 2023
Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya na shekarar 2023. Tinubu Musulmi ne daga Jihar Legas, yayin da Shettima ma Musulmi ne daga Jihar Borno, arewa maso gabashi.











