Abubakar Malami: Jerin kadarori 48 da aka ƙwace daga tsohon ministan shari'a

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
A ranar Larabar nan ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori masu alaƙa da tsohon ministan shari'ar zamani marigayi Muhammadu Buhari, Abubakar Malami, domin miƙa su ga gwamnatin tarayya.
Da take yanke hukuncin, mai shari'a Joyce Abdulmalik ta ce hukumar EFCC ta riga ta tabbatar da cewa kadarorin da aka ƙwace an same su ne ba ta halastacciyar hanya ba.
EFCC ce dai ta shigar da ƙara ta buƙatar ƙwace kadarorin tsohon ministan guda 57 na dindindin da darajarsu ta kai naira biliyan 212.8.
Sai dai kuma EFCC ta soke ƙwace wasu kadarorin tsohon ministan guda 9 da ta ce ta yi hakan ne saboda babu shaidar da ke nuna an yi amfani da kuɗaɗen da ba na halas ba wajen mallakar kadarorin da ke Kebbi da Kaduna.
Mai Shari'a Joy Abdulmalik ta ƙara da cewa Malami ya gaza gamsar da ita cewa ya mallaki kadarorin nasa ne ta hanyar halaliya.
Kafin yanzu dai mai shari'ar ta sha korar buƙatun cewa iyalan Malami ne da wasu kamfanoni suka mallaki kadarorin amma kuma kotun ta ce ita ba damuwarta waɗanda suka mallaki kadarorin ba illa hanyar da aka bi wajen samun kuɗaɗen da aka mallake su.
Mai shari'ar ta yanke hukuncin ne bisa dogaro da sashe na 17 na dokar Kuɗaɗen Haram da Laifuka Masu Alaƙa da ya bayar da ikon ƙwace kadarori.
Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta sanya ranar Alhamis ɗin nan a matsayin ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kadarori 57 da ke da alaƙa da malami.
Jerin kadarori da ke Abuja

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
- Gidan alfarma mai lamba 3011 da ke kan titin Amazon Street, a unguwar Maitama, Abuja da aka saye shi a Disamba 2022 wanda aka saya akan naira miliyan 500 kuma bayan gyara shi aka ƙimanta shi akan naira biliyan 5,950,000,000.
- Hotel mai hawa 5 da ɗakuna 53 mai lamba 683, a gundumar Jabi da ke Abuja. An saye shi a Satumbar 2020 a kan kudi naira miliyan 850,000,000 da ƙarin miliyan 300,000,000 na mallaka inda kuma bayan kammala gina shi aka ƙimanta shi a yanzu akan naira biliyan 8,400,000,000.
- Kadara mai lamba 3130 a Asokoro da ke Abuja da ya ƙunshi gidaje wanda kuma aka saya a watan janairun 2021 akan kudi naira miliyan 360,000,000.
- Otal mai ɗaki 15 da ke a lamba 3 kan titin Shrine Street da ke Maitama Abuja wanda kuma aka saya a watan Fabrairun 2018 akan kuɗi naira miliyan 430,000,000 kuma yanzu ƙimarsa ta kai naira biliyan 12,950,000,000 bayan sake gyara shi.
- Gida mai lamba 1241B da ke 11A a titin Yakubu Gowon Crescent, a Asokoro da ke Abuja wanda aka saya akan naira miliyan 325,000,000 a watan Yulin 2021.
- Shago mai lamba C52 da ke Shariff Plaza, a titin Aminu Kano Crescent da ke Wuse Abuja wanda aka saya a watan Maris na 2024, akan naira miliyan 120,000,000.
- Gida mai lamba 27, Efab Estate, 5th Avenue, 59th Crescent, Gwarimpa, Abuja. An saya a watan Janairu 2016, akan kudi naira miliyan 120.
- Fili mai lamba 13 a Ipent 7 Estate, Gundumar Karsana, Abuja. An saya a Yuni 2018, naira miliyan 85.
- Gidan duplex tare da gidan masu aiki a No. 12 Yalinga Street, kusa da Adetokunbo Ademola Crescent, Wuse II, Abuja. An saya a watan Oktoba 2018 akan naira miliyan 150.
- Rumbunan kasuwanci guda biyu B40 da B46 a Kasuwar Wuse, Abuja. An saya Yuli 2020, akan naira miliyan 50.
- Gidaje tagwaye a Zone E, Apo Legislative Quarters, Cadastral Zone B01, Plot 1401, Gundumar Gudu, Abuja. An saya daga Fabrairu zuwa Mayu 2017, akan naira miliyan 250.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Kadarorin da ke Kebbi

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
- Kadarorin da Khadimiyya for Justice and Development Initiative ta mallaka a Academic Garden City, Birnin Kebbi, waɗanda Federal Housing Authority Mortgage ta sayar. An sayi gidan daga Fabrairu zuwa Satumba 2023 akan naira miliya 187.
- Rukunun shaguna da banɗakuna da wuraren wanki da tankunan zuba ruwa na masana'antu a daura da kasuwar Birnin Kebbi. An sayi wurin a kan naira miliyan 100,000,000
- Fili mai girman hekta 100 a kan titin Birnin Kebbi zuwa Jega. An saya a shekarar 2020 akan farashi ko ƙima ta naira miliyan 100.
- Gida mai ɗakuna huɗu (bungalow) a Gesse Phase II, Birnin Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 101.
- Gidaje 9 masu ɗakuna uku (bungalow).
- Gidaje 3 masu ɗakuna biyu (bungalow) da filin Rayhaan University mai girman hekta 5.4 a Jihar Kebbi, da aka saya a kan naira biliyan 56.
- Filin wucin-gadi na Jami'ar Rayhaan mai ƙimar naira biliyan 37.8.
- Wuri na uku na Jami'ar Rayhaan. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 2.45.
- Kamfanin sarrafa kayayyakin noma na Rayhaan (Rayhaan Agro Allied Factory) a Jihar Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 490.
- Gine-ginen masana'anta. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 4.2.
- Injina da kayan aikin masana'antar. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 10.5.
- Masallacin masana'antar. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 2.45.
- Gidajen ma'aikatan Rayhaan Mill. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 1.4875.
- Ginin Rayhaan Bustan. arashi ko ƙima: Naira biliyan 3.15.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
- Azbir Arena a Jihar Kebbi.
- Otal ɗin Azbir. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 10.325.
- Maɗabba'ar buga takardu (Printing Press). Farashi ko ƙima: Naira biliyan 1.05.
- Lambuna (Gardens). Farashi ko ƙima: Naira miliyan 392.
- Masallaci. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 252.
- Kamfanin tufafi na Azbir. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 350.
- Azbir Pharmacy da Supermarket a Jihar Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 175.
- Gidan ajiyar tankokin Al-Afiya Energy da ke gaban Cibiyar Lafiya ta Jami'ar Rayhaan, a kan titin Sani Abacha Bypass, Birnin Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 2.45.
- Makarantar Rayhaan Model Academy. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 11.2.
- Makarantar Firamare da Sakandare ta Rayhaan. Farashi ko ƙima: Naira biliyan 8.75.
- Gidan tsaro na Rayhaan, kusa da titin Sani Abacha Bypass, Birnin Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 245.7.
- Gidan rediyon Rayhaan da ke kan titin Sani Abacha Bypass, Birnin Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 78.75.
- Ginin kasuwa mai hawa biyu da ba a kammala ba, wanda ke gaban Central Motor Park (Eastern Park), Birnin Kebbi.
- Tsarin gidan mai na Amasdul Oil and Gas Ltd da ke kan titin Sani Abacha Bypass, Birnin Kebbi. Farashi ko ƙima: Naira miliyan 665.
Kadarorin da ke Kano

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
- Gida mai lamba 4 kan titin Ahmadu Bello Way da ke Unguwar Nassarawa GRA, da ke birnin Kano wanda aka saya a watan Disamban 2022 akan naira miliyan 300,000,000.
- Gida mai lamba 157 kan titin Lamiɗo Crescent da ke Nassarawa GRA a Kano wanda aka saya a watan Yulin 2019.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Kadarar da ke Kaduna
- Gida mai ɗakuna huɗu tare da ɗakunan masu aiki guda biyu a No. 10B Doka Crescent, Abakpa GRA, Kaduna. An saya a Janairu 2018 akan farashi na naira miliyan 40.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK







