Ilele ya sa Autan Mamman ya ruga da gudu sau biyu

Ilele and Autan Mamman
An wallafa
Bayanan bidiyo, Ilele ya sa Autan Mamman ya ruga da gudu sau biyu

Ilele Garkuwan mai caji daga Kudu ya dambata da Autan Mamman daga Arewa a damben Lahadi a gidan wasa da ke Marabar Nyanya jihar Nasarawa, Najeriya.

Sau biyu Ilele yana sa Autan Mamman na gudu a karawar da ba ta yi kisa ba a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa, Najeriya.