Atalanta ta Italia ta sayi dan Najeriya daga RB Leipzig

Ademola Lookman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lookman ya koma RB Leipzig a 2019 amma ya yi zaman aro a kaka biyu da ta gabata a Fulham da Leicester City
An wallafa

Kungiyar Atalanta ta Italiya da ke gasar Serie A ta sayi dan wasan gaba na gefe dan Najeriya Ademola Lookman daga RB Lepzig ta Jamus a kan kudin da ba a bayyana ba.

Tsohon dan wasan mai shekara 24, na tawagar matasa ta Ingila wanda ya ci kwallo takwas a wasa 42 a zaman aron da ya yi a Leicester a bara ya amince da kwantiragin shekara hudu.

Bayan faman da ya yi na kokarin zama a Jamus, Lookman wanda ya yi zaman aro a kaka ta 2020-21 a Fulham ya ce ya yi farin cikin samun sabon gida a birnin Bergamo da arewacin Italiya.

A watan Fabrairu ne dan wasan da ya ci kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 20 da tawagar Ingila a 2017 ya koma buga wa Najeriya, kasar mahaifansa wasa.

Tsohon dan wasan na Charlton da Everton ya ci kwallo biyar a wasa 24 da ya yi wa RB Leipzig bayan da ya koma Jamus a kan kudi fam miliyan 22.5 a 2019.

Lookman ya shiga kungiyar renon 'yan wasa ta Charlton a 2014 inda nan da nan likkafarsa ta ci gaba ya samu shiga babbar tawagar kungiyar ya yi wasan farko a watan Nuwamba na 2015

A tsawon kaka biyu ya yi wa kungiyar wasa 49, inda ya ci kwallo 12, kafin ya koma Everton a kwantiragin shekara hudu da rabi a watan Janairu na 2017.

Ya ci wa Everton kwallo hudu a wasanni 48, kafin ya tafi aro RB Leipzig a kakar 2017-18, abin da sa kungiyar ta dauke shi dindindin tsawon shekara biyar a watan Yuli na 2019.

Lookman ya yi wa Najeriya wasa hudu kuma ya ci mata kwallonsa ta farko a karawar da kasar ta lallasa São Tomé and Príncipe, 10-0 a wasan neman gurbin gasar cin kofin Afirka.