Real Madrid ta bai wa Mbappe wa'adi, Man Utd ta rasa damar sayen Silva

An wallafa

Real Madrid za ta sake yunƙurin sayen Kylian Mbappe, har ma ta ba shi wa'adin zuwa tsakiyar watan Janairu mai kamawa ya yanke shawara idan zai koma can a bazara. (Athletic )

Haka kuma ƙungiyar ta Sifaniya za ta bai wa Mbappen fam miliyan 23 a duk shekara da ƙarin tukuicin fam miliyan 110 na yarda ya koma can. (Marca)

Sai dai kuma ita ma Liverpool ta shiga zawarcin Mbappen saboda yana da kyakkyawar alaƙa da kociyan ƙungiyar Jurgen Klopp. (Talksport)

Arsenal na matuƙar son Victor Osimhen na Najeriya da Napoli da ɗan wasan gaba na Bayer Leverkusen Victor Boniface shi ma ɗan Najeriya mai shekara 23 da kuma ɗan gaban Inter Milan Lautaro Martinez, na Argentina mai shekara 26, a matsayin waɗanda za ta zaba a madadin Ivan Toney na Brentford da kuma Ingila. (Express)

Manchester City ta fara tattaunawa da Juventus domin barin ɗan wasan tsakiya Kalvin Phillips ya tafi aro. (Times)

Har yanzu Chelsea na son matashin ɗan baya Pau Cubarsi, ɗan Sifaniya mai shekara 16 wanda ya taka wa tawagar Barcelona ta biyu leda a kakar nan. (Sport)

An fada wa Liverpool da Manchester United cewa matashin ɗan bayan Benfica Antonio Silva ɗan Portugal mai shekara 20 ba na sayarwa ba ne a watan Janairu. (90min)

Freiburg, da Lyon da kuma Sevilla na son ɗan wasan tsakiya na Manchester United Hannibal Mejbri, na Tunisia mai shekara 20 (Bild )

A shirye Juventus take ta yi musayar Moise Kean, ɗan Italiya mai shekara 23 don samun matashin ɗan wasan tsakiya na Arsenal Charlie-Michael Patino ɗan Ingila mai shekara 20 wanda ke zaman aro a Swansea City.(Tuttosport)

Arsenal ta sa ƙafa ta shure buƙatar Crystal Palace ta neman sayen Eddie Nketiah na Ingila mai shekara 24. (Mail)

Kociyan Arsenal ɗin Mikel Arteta zai sayar da Nketiah, da Emile Smith Rowe, da kuma mai tsaron raga Aaron Ramsdale idan ya samu tayi mai girma. (Mirror)

Tottenham za ta ƙara himma a ƙoƙarin da take yi na neman matashin ɗan bayan Genoa Radu Dragusin ɗan Romania mai shekara 21 amma kuma tana fuskantar hamayya daga Roma.(Telegraph)

Ɗan bayan Borussia Dortmund Ramy Bensebaini, na Algeria mai shekara 28, zai so tafiya Manchester United.(La Gazette du Fennec )

Kociya Andoni Iraola na fargabar cewa idan ƙungiyarsu Bournemouth ta samu cigaba to hakan fa na nufin tafiyar taurarin ƴan wasansa. Tuni daman Tottenham ke zawarcin Dominic Solanke, na Ingila. (Independent)

West Ham da Newcastle na zaman shiri bayan da ɗan gaban Napoli Giovanni Simeone, ya nuna cewa zai bar ƙungiyar a watan Janairu. (Sky Sports)