Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ba za ta iya cefane ba a Janairu, Man Utd ta bi masu son Guirassy
Arsenal na sha'awar sayen ɗan bayan Bayern Munich Matthijs de Ligt, ɗan Netherlands amma kuma ƙila ne ciniki ya tabbata a bazaran nan. (Athletic)
Arsenal ba za ta iya sayen wasu sababbin ƴan wasa ba a watan Janairu sai lalle ta rage wasu, hakan ya sa ƙila Mikel Arteta ya bayar da fifiko wajen karɓa da bayar da aron ƴan wasa. (Mirror)
Makomar Roy Hodgson a matsayin kocin Crystal Palace na cikin rashin tabbas saboda ƙungiyar na nazarin ɗauko Steve Cooper, wandda Nottingham Forest ta kora a watan nan. (Telegraph)
Wataƙila Roberto Firmino, ya bar Al-Ahli bayan wata shida da komawa ƙungiyar ta Saudiyya amma kuma wasu kungiyoyin ƙasar irin su Al-Shabab, da Al-Ettifaq da Al-Fateh, da Sheffield United da kuma wasu ƙungiyoyin na Turkiyya na sha'awarsa. (Talksport)
Ɗan wasan gaba na Guinea Serhou Guirassy, zai bar Stuttgart a watan Janairu kuma tuni AC Milan, da Manchester United da kuma Tottenham suka nuna sha'awarsu da shi. (Gazzetta dello Sport )
Liverpool za ta ƙara bayar da aron ɗan bayanta Nat Phillips a watan Janairu bayan zaman aron da ya yi a Celtic ya ƙare. (Liverpool Echo)
Crystal Palace na matuƙar son matashin dan wasan tsakiya na Sunderland, Pierre Ekwah na Faransa mai shekara 21 da kuma matashin ɗan gaban Paris St-Germain Hugo Ekitike shi ma ɗan Faransa mai shekara 21. (Standard)
Nottingham Forest ta yi nisa a tattaunawa da Monaco domin sayen ɗan gaba na gefe Gelson Martins na Portugal. (L'Equipe)
Wataƙila a cimma yarjejeniyar musaya a kan ɗan gaban Juventus Dusan Vlahovic, na Serbia mai shekara 23, da kuma Romelu Lukaku na Chelsea, wanda ke zaman aro a Roma, a shekara mai kamawa. (Tuttosport )
Borussia Dortmund na nazarin sayen matashin ɗan wasan Manchester United Dan Gore. (Football Insider)
Chelsea ta cimma yarjejeniyar sayen matashin ɗan wasan tsakiya na tawagar Senegal ta ƴan ƙasa da shekara 17, Pape Daouda Diong daga ƙungiyarsa ta Senegal, AF Darou Salam amma sai ya cika shekara 18. (Fabrizio Romano)
Juventus za ta bayar da fifikon sayen ɗan wasan tsakiya na Tottenham, Pierre-Emile Hojbjerg na Denmark a watan Janairu. (Calciomercato)
Manchester City za ta bar ɗan wasanta na tsakiya Kalvin Phillips, na Ingila ya tafi Newcastle aro, saboda ba zai amince da tafiya Juventus ba. (Talksport)
Tottenham ɗin na shirin sayen babban ɗan wasan baya watan Janairu, kuma matashin ɗan wasan Nice Jean-Clair Todibo, na Faransa shi ne a kan gaba da take so. (Teamtalk)
West Ham na son sayar da ɗan bayanta na Moroko Nayef Aguerd a watan Janairu kuma ƙungiyoyin Saudiyya na sonshi. (Football Insider)
Eintracht Frankfurt na son aron ɗan gaban Wolves Sasa Kalajdzic, ɗan Austria har zuwa ƙarshen kaka. (Bild)
Tsohon ɗan gaban Faransa Yann M'Vila na da damar sake komawa Sunderland. Ɗan wasan mai shekara 33 ba shi da ƙungiya tun bayan da ya bar Olympiakos a ƙarshen kakar bara. (Sunderland Echo)
Sevilla, da Lyon da Freiburg na son aron matashin ɗan wasan Manchester United Hannibal Mejbri a watan Janairu. (Fabrizio Romano)
Roma da ke son samun ɗan wasan baya a watan Janairu na harin ɗan bayan West Ham, Thilo Kehrer, mai shekara 27. (Corriere dello Sport)
Manchester City na dab da cimma yarjejeniyar sayen matashin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar River Plate, kuma ɗan Argentina Claudio Echeverri. (Sky Sports)
To amma matashin mai shekara 17 zai fara zama a ƙungiyar Girona ne wadda ita ma ta mai Manchester City ce, kafin nan gaba ya koma tawagar ta Guardiola. (Mundo Deportivo)