Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham ta hana Arsenal komawa ta ɗaya a Premier
West Ham United ta yi wa Arsenal kancal a ƙoƙarin da Gumnners ɗin ke yi na komawa saman teburin gasar Firimiya bayan da suka tashi wasa 2-0.
West Ham wadda ta bi Gunners har gida ta hana su rawar gaban hantsi ta fara jefa ƙwallonta ne ta hannun Tomas Soucek a minti na 13 da shiga fili.
Ɗan wasan na Jamhuriyar Czech ya ci ƙwallon ne duk da cewa alamu sun nuna bal ɗin ta fita waje kafin a kai ga cin to amma kasancewar babu cikakkiyar shedar hoton bidiyo da za ta tabbatar da hakan, cin ya tabbata.
Ɓaƙin sun ƙara ɗaga ragar abokan hamayyarsu na Landan ɗin ne bayan da tsohon ɗan bayan Arsenal ɗin Konstantinos Mavropanos ya ci da ka a minti na 55.
Duk da yawan riƙe ƙwallo da kuma hare-hare da Gunners ɗin suka yi a wasan na mako na 19 ba su iya cin ko da ƙwallo ɗaya ba.
Ita kuwa West Ham ta yi nasara jefa ƙwallo a ragar ne sau biyu a cikin hari uku ƙwarara da ta kai.
Ana dab da tashi daga wasan West Ham ta samu bugun fanareti wadda Declan Rice ya janyo, to amma mai tsaron ragar Arsenal, David Raya ya kaɗe bugun na Said Benrahma.
Sakamakon ya sa Arsenal ta ci gaba da zama ta biyu a tebur da maki biyu a bayan jagora Liverpool, mai maki 42, yayin da West Ham ta kawo ƙarshen wannan shekara ta 2023 da maki 33, makin da ba ta taɓa samu ba a tarihinta a daidai tsakiyar gasar ta Ingila.