Chelsea za ta sayo Toney na Brentford, Man United za ta ɗauko Tagliafico

 Ivan Toney

Asalin hoton, BBC Sport

An wallafa

Chelsea na iya gabatar da tayi a kan ɗan wasan Brentford, mai shekara 27, da aka yi wa kuɗi fam miliyan 80, Ivan Toney, kafin rufe kasuwar sayen 'yan ƙwallo ranar 1 ga watan Satumba. (Independent)

Tottenham ta bai wa Bayern Munich damar daukar ɗan wasan bayanta na Ingila, Eric Dier. (Sky Sports Germany)

Manchester United ta tuntubi Lyon a kan buƙatar aro ɗan wasan bayanta na ƙasar Argentina, Nicolas Tagliafico. (Le Parisien)

Besiktas ta shirya bai wa ɗan ƙwallon gaban Manchester United mai shekara 21 daga Ingila, Mason Greenwood, damar ci gaba da buga ƙwallo, bayan an sanar da cewa zai bar filin wasa na Old Trafford. (i Sport)

Manchester United kuma ta miƙa tayin ɗauko aron ɗan wasan bayan Sifaniya, Marc Cucurella, mai shekara 25 daga Chelsea. (Athletic)

Bayern Munich ta miƙa wa Chelsea buƙatar neman ɗan ƙwallon tsakiyar Ingila, mai shekara 23, Conor Gallagher. Haka shi ma ɗan wasan baya mai buga wa ƙungiyar Ingila ta ‘yan ƙasa da shekara 21 Trevoh Chalobah, yana da damar tafiya kulob ɗin zakarun na Gasar Bundesliga ta Jamus. (talkSPORT)

Haka kuma, Chelsea na duba yiwuwar sake dawo da ɗan wasan gaban Atletico Madrid na ƙasar Portugal, Joao Felix, bayan zaman aro da matashin mai shekara 23 ya yi a filin wasa na Stamford Bridge bara. (90 min)

Aston Villa na tattaunawa da Barcelona kan yarjejeniyar ɗaukar ɗan ƙwallon bayan Faransa, mai shekara 28, Clement Lenglet. (Fabrizio Romano)

Fulham ta yi nisa a tattaunawa da Everton wajen ɗaukar ɗan ƙwallon tsakiya na Najeriya mai shekara 27, Alex Iwobi. (talkSPORT)

Haka zalika, Fulham ɗin ta amince da yarjejeniya da kulob ɗin Sevilla kan ɗan wasan gaban Argentina, mai shekara 29, Lucas Ocampos. (Telegraph)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana kuma ganin akwai ƙarin yiwuwar cewa West Ham za ta gabatar da tayin kwanturagi na taƙaitaccen lokaci ga tsohon ɗan wasan tsakiyar Ingila, mai shekara 30, Jesse Lingar, wanda a yanzu ba shi da yarjejeniyar kowa a kansa. (Standard)

Nottingham Forest ta amince da yarjejeniyar ba da aron ɗan wasan bayanta daga ƙasar Portugal, Nuno Tavares, ɗan shekara 23, ga Arsenal. (Fabrizio Romano)

To amma Arsenal ɗin ta yi watsi da buƙatar Chelsea da ke neman ɗaukar ɗan wasan gabanta na Ingila, mai shekara 23, Emile Smith Rowe. (Mail)

Ita kuwa, Wolves tana nazari a kan yiwuwar ɗauko ɗan ƙwallon ƙungiyar Club Libertad na ƙasar Paraguay mai shekara 18, Enso Gonzalez. (Football Insider)

West Ham na tattaunawa da Paris St-Germain don sayen ɗan wasan gaba na Faransa mai shekara 21, Hugo Ekitike. (Sky Sports)

Ita ma, Crystal Palace ta miƙa tayin karɓo aron Ekitike ɗin. (L'Equipe)

Luton na ɗokin cimma yarjejeniya don karɓo aron ɗan ƙwallon bayan Arsenal, mai shekara 27, Rob Holding. (Standard)

Ɗan wasan Liverpool na Ingila, Nat Phillips zai iya barin ƙungiyar kafin ƙarshen lokacin hada-hadar sayen ‘yan wasa, inda Middlesbrough ke cikin kulob-kulob da ke sha’awar ɗaukar ɗan ƙwallon mai shekara 26 matsayin aro. (Athletic)