Everton ta kammala sayen Beto daga Udinese

Beto

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Everton ta kammala daukar dan wasan gaban Portugal, Beto daga Udinese ta Italiya kan kudi fam miliyan 30.

Dan wasan mai shekaru 25 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu a Goodison Park, kuma ya zama dan wasa na biyar da suka dauko a wannan bazaran.

Dan wasan ya ci wa Udinese kwallaye 10 a kakar wasan da ta wuce kuma ya karfafa kungiyar Toffees da har yanzu ba ta kai ga zura kwallo a raga ba a wannan kakar wasan.

Kungiyar Sean Dyche ita ce ta karshe a teburin Premier, bayan da ta yi rashin nasara a wasanni ukun farko.

Za su kara da Doncaster Rovers a gasar Carabao cup ranar Laraba kafin tafiya zuwa Sheffield United a gasar Premier League ranar Asabar.

Tuni dai Dyche ya dauko dan kasar Beto Youssef Chermiti daga Sporting Lisbon kan kudi fam miliyan 15.

Dan wasan mai shekaru 19 ya fara buga wasansa na farko a karawa da Wolves ta doke su da ci 1-0 a ranar Asabar.

Kulob din na Merseyside ya kuma kulla yarjejeniya da Ashley Young a matsayin kyauta da kuma 'yan wasan gaba Arnaut Danjuma da Jack Harrison a matsayin aro.