Pillars za ta fara zuwa gidan Sunshine a Firimiya 2023/24

Nigerian Premier League

Asalin hoton, Kano Pillars Twitter

An wallafa

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya ta fitar da jadawalin wasannin kakar bana ta 2023/24.

An raba jadawalin wasannin bana a babban birnin tarayya Abuja da za a fara gasa ta 53 ranar 9 ga watan Satumbar 2023.

Kungiyar Enyimba ce mai rike da kofin bara kuma na tara jimilla, wadda take fatan ta farko daza ta lashe babban gasar tamaula ta Najeria karo na 10.

Kungiyoyi 20 ne za su kece raini a bana da suka hada da 16 da suka kara a bara da kuma hudun da suka samu buga gurbin kakar 2023/24.

Kungiyoyin da suka hauro gasar bana sun hada da Heartland da Sporting Lagos, da Kano Pillars da kuma Katsina United.

Wannan shine karon farko da Sporting Lagos za ta fafata a gasar Firimiya ta Najeria a tarihi.

Kungiyoyi hudun da suka bar gasar bara sun hada da Wikki Tourists da Nasarawa United da El-Kanemi Warriors da kuma Dakkada da za su buga Nigeria National League.

Jadawalin wasannin bana;

  • Enyimba da Bendel Insurance
  • Heartland da Lobi Stars
  • Sunshine Stars da Kano Pillars
  • Katsina United da Kwara United
  • Abia Warriors da Niger Tornadoes
  • Ranagers International da Doma United
  • Rivers United da Remo Stars
  • Bayelsa United da Akwa United
  • Sporting Lagos da Gombe United
  • Shooting Stars da Plateu United