Rubiales ya ajiye muƙamin shugaban ƙwallon ƙafar Sifaniya bayan shan matsi

Asalin hoton, Getty Images
Luis Rubiales ya ajiye aikin shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, bayan da ake ta caccakarsa sakamakon sumbatar ƴar wasa Jenni Hermoso a leɓe da ya yi a gasar cin kofin duniya ta mata.
Hermoso, mai shekara 33, ta ce ba tare da amincewartar ya sumbace ta a leɓe ba, ta kuma shigar da ƙara ranar Talata.
Rubiales ya ce ya miƙa takardar ritaya ga shugaban hukumar ƙwallon kafa ta Sifaniya na riƙon ƙwarya, Pedrp Rocha.
''Ba zan iya ci gaba da aikina ba,'' kamar yadda ya sanar da Piers Morgan a wata hirar talabijin.
Haka kuma, Rubiales, mai shekara 46 ya ajiye muƙamin mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Turai wato Uefa.
Sifaniya ta doke Ingila da ci 1-0 a wasan karshe a Australia, sai dai batun sumbatar ya danne bajintar lashe kofin duniya da gudanar da murnar daukar kofin a kasar.
Ranar Juma'a masu shigar da kara suka shigar da tuhuma ga kotu - bayan da Hermoso ta tabbatar a ranar Talata cewar Rubiales ya ci zarafin ta da keta mata mutunci.
Rubiales ya dage cewar da amincewarta ya sumbace ta a leɓe - wanda tuni hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da shi.
Tsohon shugaban ya ce yana fatan barin sa aikin zai ƙara ƙarfafa zawarcin da Sifaniya ke yi na hadakar karbar bakuncin gasar kofin duniya tare da Morocco da Portugal a 2023.














