Mahaifiyar Rubiales ta fara yajin kin cin abinci

Asalin hoton, Getty Images
Mahaifiyar shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales ta shiga yajin kin cin abinci saboda cece-ku-ce da ake yi dangane da sumbar 'yar wasa da ya yi.
Ana ta sukar Rubiales, mai shekaru 46, bayan ya sumbaci 'yar wasan gaba Jenni Hermoso a lebe, bayan wasan karshe a gasar cin kofin duniya na mata a Sydney.
Mahaifiyarsa, Angeles Bejar, yanzu ta kulle kanta a wani coci a Motril.
Ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Sifaniya EFE cewa yajin kin cin abincin zai ci gaba ''dare da rana”.
Hermoso, mai shekaru 33, ta ce ba ta amince da sumbar da Rubiales ya yi mata a lokacin bikin gabatar da su a Sydney a ranar 20 ga Agusta ba.
Rubiales ya sha alwashin ba zai yi murabus ba a ranar Juma'a amma hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da shi ranar Asabar.







