Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
City na son Guimaraes, Sancho ba ya son komawa Man Utd
Ɗanwasan baya na Everton da Ingila Jarrad Branthwaite mai shekara 21 na cikin lissafin farko na Manchester United da take son ɗaukowa a bazara. (Star)
Ɗanwasan gaba na Crystal Palace da Faransa Michael Olise, mai shekara 22, shi ma yana cikin lissafin United a bazara. (Football Transfers)
United za ta nace kan Branthwaite, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 75 a Everton ko da kuwa babu tabbas kan makomar Erik ten Hag. (Mirror)
Manchester City na sha'awar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil mai shekara Bruno Guimaraes, kuma duk wanda zai saye shi sai ya biya fam miliyan 100. (Football Transfers)
Tottenham ta shiga hamayya da Manchester City da Liverpool da Newcastle da kuma Arsenal kan ɗanwasan Wolves da Portugal Pedro Neto mai shekara 24. (Football Insider)
Kocin Jurgen Klopp mai barin gado ya ba da shawarar ɗauko ɗanwasan baya na gefen hagu na Algeria Rayan Ait-Nouri daga Wolves, kodayake ɗanwasan na cikin jerin ƴanwasan da Manchester United ke farauta. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Ingila Jadon Sancho, mai shekara 23 ba ya da ra'ayin dawowa Manchester United bayan cikar wa'adin yarjejeniyarsa Borussia Dortmund a matsayin ɗanwasan aro inda ya ɗora laifin taɓarɓarewarsa ga Erik ten Hag. (Bild, via 90min)
Dortmund na son Sancho ya ci gaba da taka mata leda inda take tunanin musaya tsakaninta da United, matakin da zai ba ɗanwasan gaba na Netherlands Donyell Malen, zuwa Old Trafford. (Fichajes - in Spanish)
Tsohon daraktan wasanni na Roma Tiago Pinto, wanda ya yi aiki da Jose Mourinho a ƙungiyar ta Italiya ya ce yana son ya gaji Dan Ashworth a Newcastle wanda zai koma Old Trafford. (i Sport - subscription required)
Ɗanwasan baya na Portugal Joao Cancelo, mai shekara 29, ya ce yana fatan tabbatar da zamansa a Barcelona daga Manchester City maimakon ɗanwasan aro. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Chelsea na cikin ƙungiyoyin da ke sa ido kan ɗanwasan tsakiya na FC Nordsjaelland da Ivory Coast Mario Dorgeles, mai shekara19. (Tipsbladet - in Danish)
Tottenham za ta bar ɗanwasan baya na Wales Joe Rodon, mai shekara 26, ya ci gaba da taka leda a Leeds United a bazara maimakon ɗanwasan aro. (Football Insider)