Foden zai ƙara daraja a City, PSG ta ware manyan kuɗi kan Yamal

An wallafa

Ɗanwasan tsakiya na Ingila Phil Foden, mai shekara 23, na shirin soma tattaunawa da Manchester City kan sabunta kwantaraginsa inda zai kasance ɗaya daga cikin ƴanwasan da suka fi karɓar albashi a ƙungiyar. (Football Insider)

City ta shiga sahun masu farautar ɗanwasan gaba na Portugal Pedro Neto, mai shekara 23, inda take hamayya da Liverpool da Newcastle da Arsenal kan ɗanwasan da darajarsa ta kai fam miliyan 60 a Wolves. (Telegraph - subscription required)

Manchester United na son ɗauko matashin ɗanwasan baya na gefen hagu a bazara. (Fabrizio Romano)

United kuma na son ɗauko matashin ɗanwasan Faransa mai shekara 18 Leny Yoro daga Lille kuma za ta biya kuɗi kusan fam miliyan 41kan ɗanwasan. (Teamtalk)

Tottenham na nazarin shiga hamayya da Arsenal da Chelsea kan ɗanwasan Athletic Bilbao da Spain mai shekara 21 Nico Williams. (Mirror)

Spurs na fatan kaftin ɗinta Son Heung-min, mai sherkara 31 zai amince ya sabunta kwantaraginsa. Yarjejeniyar ɗanwasan mai shekara za ta kawo ƙarshe a 2025. (Give Me Sport)

Tattaunawa tsakanin ɗanwasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher mai shekara 24 da Chelsea ta gamu da cikas saboda dalilai na kuɗi a ƙungiyar. (Football Insider)

Liverpool da Arsenal sun nuna sha'awar ɗanwasan tsakiya na Fulham da Portugal Joao Palhinha amma har yanzu Bayern Munich ba ta haƙura da ɗanwasan ba mai shekara 28. (Teamtalk)

Liverpool za ta sanar da dawo da Michael Edwards a mako mai zuwa tare da Richard Hughes a matsayin daraktan wasanni. (Sky Sports)

Brentford sai ta rage farashin da ta aza kan ɗanwasanta na Ingila Ivan Toney don kada ta kori Arsenal da Chelsea da ke son ɗanwasan mai shekara 27. (Mirror)

AC Milan na sa ido kan ɗanwasan baya na Fulham da Ingila Tosin Adarabioyo, mai shekara 26, idan kwangilar shi ta kawo ƙarshe a bazara. (Calciomercato - in Italian)

Paris St-Germain a shirye take ta biya Barcelona yuro miliyan 200 domin ɗauko matashin ɗanwasan gaba Lamine Yamal, mai shekara 16. (Marca - in Spanish)

An ba Newcastle damar ɗauko ɗanwasan tsakiya na Ivory Coast Mario Dorgeles daga Nordsjaelland. (Chronicle)