Man Utd na son yin wuf da Osimhen, za ta sayar da Sancho

An wallafa

Manchester United da Paris St-Germain sun kasance a sahun gaba da ke farautar ɗanwasan gaba na Napoli da Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 25. (The Independent)

Newcastle United na dab da amincewa da sabuwar yarjeniya da Joelinton, yayin wa'adin kwangilar ɗanwasan mai shekara 27 na Brazil ta rage sama da shekara ɗaya. (Telegraph - subscription required)

Tottenham Hotspur ta shiga farautar ɗanwasan Sporting Lisbon Morten Hjulmand - ɗanwasan tsakiya mai shekara 24 na Denmark wanda ya zana tambarin Arsenal a kafaɗarsa. (Record, via Sun)

Chelsea ta yanke shawara kan kocin Brighton Roberto de Zerbi da Ruben Amorim a matsayin waɗanda za su maye gurbin Mauricio Pochettino. (Guardian)

Wasu ƴanwasan Manchester United sun yi imanin ƙungiyar za ta sallami kocinta Erik ten Hag idan an kammala kaka. (Daily Mail)

Kocin Tottenham Ange Postecoglou zai yi watsi da duk wani tayi na barin ƙungiyar a bazara - haɗi da tayin Liverpool. (Football Insider)

Manchester United na son sayar da ɗanwasan gaba Jadon Sancho a bazara wanda ta ba Borussia Dortmund aro, ko da kuwa Erik ten Hag kocin ƙungiyar. (Football Insider)

Newcastle na nazarin bayar da aron ɗanwasan Gambia mai shekara 19 Yankuba Minteh. Yanzu haka Minteh yana taka leda a Feyenoord a matsayin aro. (the i)

Liverpool sai ta biya Bayer Leverkusen fam miliyan 21 idan tana son ɗauko Xabi Alonso zuwa Anfield a bazara - kuɗin ya lunka wanda ta saye shi lokacin da yana taka leda. (Mirror)

Real Madrid a shirye take ta ƙara kuɗi kan tayin da ta yi wa ɗanwasan baya na Bayern Munich da Canada Alphonso Davies, mai shekara 23, zuwa fam miliyan 43m. (Cadena Ser, via Mundo Deportivo)

Kocin Burnley Vincent Kompany na ci gaba da samun goyon bayan ƙungiyar duk da fuskantar ƙalubale na taɓarɓarewar abubuwa bayan shan kashi hannun Bournemouth ranar Lahadi. (Athletic)

Chelsea ta aika da wakilai domin sa ido kan matashin ɗanwasan Ingila Archie Brown, da ke taka leda Gent ta Belgium. Leeds United da West Ham United ma na sa ido kan tsohon ɗanwasan na Derby County. (HITC)