Abubuwan da shugabannin kasashen duniya ke cewa a kan rasuwar Sauraniya Elizabeth ta II

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin kasashen duniya da sauran jami’an diflomasiya na ci gaba da nuna alhinin game da mutuwar Sauraniya Elizabeth ta II, wacce ta rasu tana da shekara 96 a duniya.
Sun yaba da yadda ta saudakar da kai wajen gudanar da aikinta da jajircewarta da kuma kasancewarta mai fara’a da kyautatawa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya jagoranci shugabannin da suka nuna alhini inda ya tuna da “Sarauniya a matsayin mai kirki” wacce ta kasance abokiyar Faransa”.
Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya ce Sauraniya ta ja hankalin kasashen duniya a kan yadda ta rika mulki kuma ta rika aiki ba dare ba rana.
"Sau da yawa mun rika ganin yadda take mu’amala da mutane inda take magana da su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da raha,” a cewar Mr Obama, wanda ya gana da sarauniya a lokuta da dama.
Shugaban Amurka na yanzu Joe Biden ya bayyana Sarauniyar a matsayin sarauniyar da ta kafa “tarihi a zamanin nan.”
Da yake magana a kan ziyararsa a Birtaniya a shekarar 2021 a matsayin shugaban kasa, Mista Biden ya ce “ ta nuna mana hazakarta da kirkinta da kuma hikimarta.”
Sarauniya Elizabeth ta biyu ta gana da shugabannin Amurka 14 a lokacin mulkinta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ce " ba zan taba mantawa da kyakkyawar abota da martaba da hikima da kuma ban dariyarta.
"Mace ce mai kyau- babu kamarta!,” kamar yadda ya bayyana a sakon da ya rubuta a shafinsa na Truth Social.
Haka kuma a lokacin mulkinta ne firaiministoci 12 na Kanada suka yi mulki.
A jawabinsa jim kadan bayan da aka ba da labarin rasuwarta, Justin Trudeau ya ce mutanen Canada suna nuna alhininsu.
“Ta kasance daya daga cikin mutanen da na fi so a duniya, kuma za mu yi kewarta”, in ji shi.
'Sauraniya ce da babu kamarta '
Sarki Netherlands Willem-Alexander - wanda dan uwan sarauniya Elizabeth na biyar ne - ya ce shi da sarauniya Maxima za su tuna da ita a matsayin “Sarauniya mai hikima, mai matukar girmamawa da kauna”.
Shi ma Sarki Philippe da Sarauniya Mathilde na Belguim sun ce “shugaba ce da kasafai ake ganin irinta ba wacce a tsawon lokacin da ta shafe kan mulki ta nuna mutunci da jajircewa da sadaukarwa”.
Firaiministan Indiya Narenda Modi ya tuna da taron da ba zai taba mantawa da shi ba da sarauniya a ziyararsa zuwa Birtaniya
"Ba zan manta da karamcinta ba da kyautatawarta,” kamar yadda ya bayyana a sakon da ya wallafa a shafin Tuwita.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jinjina wa Sauraniyar yana mai cewa “aniyar da ta nuna wajen ganin Jamus da Birtaniya sun sasanta bayan abubuwa masu tayar da hankali da suka faru a lokacin Yakin Duniya na Biyu abu ne da ba za a manta da shi ba.”
An samu gagarumin sauyi a mulkinta
A matsayinta na sarauniyar da ta shafe shekara 70 kan mulki Sarauniya Elizabeth ta yi rayuwa a cikin wani lokaci na sauyi kamar yadda aka bayyana a sakonin ta’aziyya.
Kamar yadda Barack Obama ya bayyana “ta yi rayuwa a lokutan wadata da rikice-rikice kama daga lokacin da bil adama ya sauka a wata da kuma faduwar katangar Berlin”.
Sakatare janarar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce a zamanin mulkinta ne aka samu gagarumin sauyi ciki har da bai wa kasashen Afrika da Asiya ‘yancin kai da kuma farfadowar kungiyar Commonwealth”.
“Sadaukarwar da ta yi ta tsawon rayuwarta wajen yi wa al’ummarta hidima abar sha’awa ce”
Shugaban Isra’ila Isaaz Herzog ya ce duk da cewa an samu gagarumin sauyi a lokacin mulkinta amma duk tsawon wannan lokaci “ta kasance abar koyi mai nagarta, mai rikon amana mutuntaka da kishin kasa.”
Ko da yake Sarauniyar ba ta ziyarci Isra’ila ba, Charles, Edward, William da marigayi Philip – wanda aka binne mahaifiyarsa a birnin Kudus, sun je.
"Sauraniya Elizabeth ta kafa tarihi kuma ko a mutuwarta ma ta bar abubuwa da za a yi koyi da su,”a cewar Shugaba Herzog.












