Man Utd ta cimma sabuwar yarjejeniya da Diallo, Arsenal na harin Mbeumo

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Danwasan gaba na gefe na Ivory Coast Amad Diallo, mai shekara 22, ya amince da yarjejeniyar da ke kunshe a cikin sabon kwantiragi da Manchester United. (ESPN)

Danwasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 19, da kuma na Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20, dukkanninsu za su ci gaba da zama a Manchester United, duk da damuwar da ake nunawa ta saba dokokin da United ta yi na harkar kudade (PSR) . (Sky Sports)

Haka kuma Manchester United na bukatar ta sayar da wani ko wasu 'yanwasa domin ta samu yuro miliyan 60 (£50m) na sayen dan bayan Portugal da Paris St-Germain Nuno Mendes, mai shekara 22. (Independent)

Dan wasan gaba na Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, na cikin jerin 'yanwasan da Arsenal ke son saye a bazara. (Florian Plettenberg)

Kungiyoyin Jamus - Bayer Leverkusen, RB Leipzig, Mainz, Borussia Dortmund da kuma Stuttgart, dukkanninsu na neman matashin danwasan tsakiya na Mannchester City, kuma dan tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 James McAtee, mai shekara 22. (Telegraph)

Har yanzu Manchester City na son Omar Marmoush mai shekara 25 da aka yi wa kudi fam miliyan 50, amma kuma kila sai ta dage ta raba dan gaban na Masar da Eintracht Frankfurt a watan Janairu saboda kungiyar ta Jamus na kokarin ganin ta samu gurbin gasar Zakarun Turai ta - Champions League. (Guardian)

Haka kuma Man City din na nazarin sayen dan bayan Nottingham Forest da Najeriya Ola Aina, mai shekara 28. (GiveMeSport)

Manchester United na sane da cewa wakilan Marcus Rashford, na tattaunawa da AC Milan. (Sky Sports)

Cristiano Ronaldo na son sake hadewa da tsohon abokin wasansa a Manchester United - Casemiro, mai shekara 32, kuma tuni ya bukaci Al-Nassr ta nemi daukar dan wasan na tsakiya na Brazil. (Mirror)

Tattaunawa ta yi nisa da Manchester City ke yi a cinikin dan bayan Uzbekistan Abdukodir Khusanov, mai shekara 20, a cinikin da ya kai fam miliyan 30 da kungiyarsa ta Lens. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na gefe na Brazil Antony, mai shekara 24, ya yi watsi da bukatar tafiya kungiyar Olympiakos ta Girka, amma kuma har yanzu yana son barin Manchester United. (Mirror)