Ƙungiyar Barau FC ta dakatar da koci Salisu Yusuf

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mahukuntan ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barau FC ta sanar da dakatar da kociyanta, Salisu Yusuf nan take.

Ta dauki wannan matakin ne, bayan kammala taron da mahukuntan suka gudanar kan tsohon wanda ya harar da Super Eagles.

A wata takardar da ta gabatar ɗauke da sa hannun jami'in dake kula da yaɗa labaran ƙungiyar, Ahmad Hamisu Gwale ta godewa Yusuf kan aikin da ya gudanar.

Tuni aka sanar da mataimakinsa, Rabiu Tata a matakin wanda zai yi aikin rikon ƙwarya a Barau FC mai buga Nigerian National League (NNL) 2024/2025.

Yusuf wanda ya fara aiki kafin fara kakar bana, ya ja ragamar wasa huɗu a gasar tamaula mai daraja ta biyu a Najeriya.

A cikin karawar ya yi canjaras biyu a gida aka doke Barau FC fafatawa biyu da ta yi a waje a gasar ta Najeriya.

Ya karɓi aiki wata biyar da suka wuce, wanda ya horar Nasarawa United da Dolphins FC da Kano Pillars.

Ya yi mataimkin Samson Siasia da Stephen Keshi a tawagar Najeria, ya kuma horar da Enyimba da El-Kenemi Warriors da kuma Super Eagles.