Wane ne sabon kocin Najeriya, Éric Chelle?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talata ne hukumar ƙwallon ƙafar Najeriya, NFF ta tabbatar da ɗaukar Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallan ƙafar ƙasar, Super Eagles.

Naɗin Chelle ya fara aiki ne nan take kamar yadda sanarwar NFF ta nuna.

Hukumar ta NFF ta ce ta yanke shawarar ɗaukar sabon kocin ne daga ƙetare a zaman da ta yi ranar 2 ga watan Janairun 2025.

NFF ta ce babban aikin da ta ɗora wa tsohon kocin ɗan asalin ƙasar Mali shi ne: kai Najeriya Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Abin da muka sani game da Éric Sékou Chelle

Ba kamar sauran fitattu a harkar ƙwallon ƙafar Afirka, irin su George Weah da Abedi Pele da Samuel Eto'o da Rashidi Yekini da sauransu ba, Eric Chelle ba fitacce ba ne a ƙwallon ƙafar Afirka.

Dalili kuwa shi ne a lokacin da yake ɗan wasa bai wani shahara sosai ba.

A lokacin da yake taka-leda, sau biyar kawai ya buga wa babbar tagawar ƙwallon ƙwallon ƙafar ƙasarsa, Mali wasa.

Dangane da matakin ƙungiyoyi kuwa, ya taka leda ne yawanci a ƙananan ƙungiyoyin Faransa, irin su Martigues da Valenciennes da Lens da Istres da kuma Chamois Niortais.

To sai dai Chelle ya bai wa mutane da dama mamaki a matakin koci saboda irin ƙoƙarin da ake ganin ya yi.

Kafin ya zama kocin babbar tawagar Mali, ya riƙe wasu ƙungiyoyin Faransa da ke buga ƙaramar gasar ƙasar.

Mai shekara 47 ya samu ƙwarewa a aikin horaswa ne a ƙungiyoyin GS Consolat, FC Martigues, MC Oran and Boulogne.

A shekarar 2022 ne Mali ta naɗa shi a matsayin wanda zai jagoranci babbar tawagar ƙasar, kuma ya bayar da mamaki bayan ya kai ƙasar gasar cin Kofin Afirka ta 2023 da aka gudanar a Ivory Coast.

A gasar ne, Mali ta samu nasarar kaiwa matakin kwata-fainal, kafin mai masaukin baƙi ta fitar da ita a ƙarin lokaci.

Bayan gasar ne ƙasar ta kore shi a watan Yunin 2024.

'Riƙe Super Eagle ba ƙaramin aiki ba ne'

Aikin horas da Najeriya babban aiki ne da ke buƙatar ƙwarewa da jajircewar koci, la'akari da yadda ƙasar ke da fitattun ƴanwasa da ke taka-leda a wasu manyan ƙungiyoyin Turai.

To amma duk da ƙwararrun ƴan wasa da ƙasar ke da su, tana fama da matsalar samun nasarorin da ake buƙata a wasanninta, musamman a Afirka.

Mutane da adama na alaƙanta rashin kataɓus da Super Eagle ke yi da rashin ƙwararren koci, wanda zai iya haɗa fitattun ƴan wasan da ƙasar ke da su domin haɗa tawaga mai ƙarfi.

Kociyoyi da dama - na ciki da wajen ƙasar - sun zo, sun kuma tafi, amma babbar tambayar da ke waɗari a bakunan ƴan ƙasar, ita ce shin Eric Chelle zai iya fitar wa Super Eagles kitse daga wuta?

Cikin sanarwar naɗin nasa, NFF ta ɗora masa alhakin kai Najeriya gasar Kofin Duniya.

A yanzu haka ƙasar na matsayi na biyar a kan teburin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da maki uku, bayan da ta ji jiki a hannun Benin da Lesotho.

Wasannin farko da Chelle zai fuskanta a neman gurbin Gasar Kofin Duniya ta 2026 su ne a watan Maris inda za ta buga wasa biyu.

A yanzu hankula sun koma kan sabon kocin domin ganin irin rawar da zai taka wajen farfado da Super Eagles.