Indonesia ta naɗa Kluivert sabon kociyanta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Indonesia ta sanar da ɗaukar tsohon ɗan wasan tawagar Netherlands da kungiyar Barcelona, Patrick Kluivert a matakin sabon kociyanta.

Mai shekara 48 ya maye gurbin ɗan kasar Korea ta Kudu, Shin Tae-yong - kenan an ɗora masa alhakin kai tawagar gasar kofin duniya da kasashe 48 za su kara a 2026.

Kluivert, ya lashe Champions League a matakin ɗan wasa a Ajax, wanda ya buga gasar Premier League a Newcastle United.

Ya amince da ƙunshin ƙwantiragin kaka biyun da aka gabatar masa da cewar za a iya tsawaita masa da zarar ya yi abin kirki.

Indonesia ta taɓa buga babbar gasar tamaula ta duniya a 1938.

Ɗan kasar Netherlands zai fara aiki da wasan neman shiga gasar kofin duniya da zai fuskanci Australia a watan Maris.

Tawaga biyu ce za ta kai gasar kofin duniya kai tsaye daga shida da suke gumurzu a rukuni, yayin da ta uku da ta huɗu za su je buga karawar cike gurbi.

Indonesia, wadda take ta 127 a jerin waɗanda ke kan gaba a ƙwallon kafa a duniya a jerin jadawalin Fifa, tana ta uku a cikin rukuni bayan karawa 10.

Ƙungiya ta karshe da Kluivert ya horar ita ce Adana Demirspor, wadda ya yi wata biyar a 2023.

Ya ja ragamar Curacao ya kuma yi mataimakin Louis van Gaal da Clarence Seedorf lokacin da suka ja ragamar Netherlands da kuma Kamaru.