Najeriya ta bullo da tsarin koyarwa da harsunan gida a firamare

Najeriya
Bayanan hoto, Harsunan Gida
An wallafa

Majalisar ministoci ta gwamnatin Najeriya ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan kasar wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar.

 

Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka  ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro.

 

Ministan ya bayyana cewa ” ka'idojin koyarwa na shekaru shida na farko a makaruntun firamare za su kasance cikin harshen gida.”

 

Tun kafin  Najeriya ta samu 'yancin-kai daga Birtaniya take amfani da Ingilishi  a matsayin  harshen hukuma inda cibiyoyin  ilimi a kowa ne mataki suke amfani da shi a matsayin harshen gama-gari na koyarwa.

 

Haka kuma wasu al’ummomi  na amfani da harsunan gida  tare da Ingilishi  a azuzuwa.

 

A yanzu mahukunta sun ce za a fi ba harsunan gida fifiko a makarantun  firamare.

A cewar ministan ilimin  Najeriya: ''Yara sun fi koyon abu da sauri, idan aka koyar da su a cikin yarensu na gida.”

'Tsari ne mai kayu amma akwai Kalubale'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ministan Ilimin  ya amince cewa aiwatar da sabon tsarin na iya zama kalubale domin,  “ yana bukatar aiki tukuru wajen samar da kayayyakin koyarwa da malaman da za su yi wannan aiki da sauransu.”

 

Wani kalubale da za a iya fuskanta shi ne  yawan harsunan da ake amfani da su  a  Najeriya, wadanda sun kai 625 a cewar mahunkan kasar.

Wannan na nufin cewa zabar yarukan da za a yi amfani da su na iya zama wani abu mai wahala a kasar da ta fi yawan al’umma a Afirka.

Ministan  ya ce ba za a takaita koyarwar a kan manyan harsuna uku na kasar ba

 ‘’Akwai harsuna 625 a Najeriya kuma idan muka sami kayayyakin koyarwa, za a rika koyar da makarantu da ke kowa ce al’umma da harsunan gida, kuma ba za mu takaita koyarwar  ga manyan harsunan kasarnan uku ba wato Hausa da Ibo da na Yarabanci”.

 

“ Sannan yayin da ake koyar da su darussa cikin  harsunan iyayen nasu, za a kuma ba su damar koyon wasu harsunan Najeriya da suke sha’awa, baya ga koya musu manyan harsunan kasa da kasa kamar Turancin Ingilishi da Faransanci da Larabci da sauransu” in ji shi.

 

Sai dai babu cikakken bayani a kan lokacin da sabon  tsarin zai soma aiki.

Mahukuntan ilimi a Najeriya sun ce da farko za su so su fara samar da kayayyakin  koyarwa da malaman harsunan na gida kafin shirin ya soma aiki gadan-gadan.