Yadda ‘yan bindiga ke sanya haraji ga jama'a a jihar Katsina

Asalin hoton, others
Al'ummomin wasu garuruwa shida na yankin ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, sun ce suna cikin halin ƙaƙa-nika-yi, sakamakon harajin naira miliyan goma da ƴan bindiga suka ƙaƙaba masu, baya ga hare-haren da ƴan bindigan ke yawan kai wa garuruwan, suna kuma sace mutane don neman kudin fansa tare da kwasar dabbobi da sauran dukiyoyi.
Wata majiya ta shaida wa BBC, cewa yanzu haka akwai mutum fiye da 20 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su, tare da neman biya kudin fansa.
Bayanan da BBC ta tattara sun ce ƴan bindigan suna hana jama'ar garuruwan da abin ya shafa sakat, har abin ya kai ga hana jama'a zuwa aiki a gonaki. wani mutumin yankin, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya bayyana irin halin da suke ciki:
‘‘Da dare ba ka bacci, da rana ba ka zuwa gona, rayuwa na cikin matsala. Halin da muke ciki ma sun yanka mana haraji, na miliyn 10, sai mun haɗa ta...duk mai mata abin da zai bada 21, 500.’’
Mutumin ya ce kusan kullum sai ƴan bindigar sun yi wani nau’in cin mutumci ga jama’a, ko dai a gonaki ko a gida.
Yayin da muka tuntubi Dokta Nasiru Mua'azu, kwamishinan tsaro na jihar ta Katsina, ya yi bayani cewa akwai wani lokaci da ƴan bindigar suka fafata da sojoji kuma har ta kai ga sojojin sun fatattake su tare da ƙwace masu babura, don haka ‘‘ina zargin ramuwar gayya ce ƴanbindigar ke yi a kana jama’a.
Dokta Mu’azu ya ce gwamnati na yin bakin ƙoƙarin ta domin magance wannan matsala, amma a mastayin wani mataki na wucin gadi, inda ‘’jami’an tsaro ke yi wa manoma rakiya har zuwa gonaki da kuma tashin su, na tsawon wata guda. ‘’
Ya ƙara da cewa ‘’Ita gwamnatin jihar Katsina ba za ta lamunci irin wannan ba kuma kullum haka yake, kuma kullum in shaa Allah za mu ci gaba da kare al’ummar mu’
Ire-iren wadannan matsaloli da jama'ar wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina ke fama da su, nuni cewa har yanzu da sauran rina a kaba game da matsalar tsaro da ke ke addabar yankin arewa maso yammacin Najeriya, duk kuwa da kokarin dakile ta hukumomi ke ta bayar da tabbacin suna yi.










