Xavi na son dauko Raphinha idan ya karɓi Man U, Guardiola ya bukaci a ɗakko masa Lukeba

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na zawarcin dan wasan gaban Sweden Viktor Gyokeres, Xavi na son dauko Raphinha daga Barcelona idan ya zama kocin Manchester United,
Manchester City na zawarcin dan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, a matsayin wanda zai maye gurbin Erling Haaland na dogon lokaci. (Sky Sport Switzerland)
Tsohon kociyan Barcelona Xavi yana son daukar dan wasan gaban kulob din Catalonia na Brazil Raphinha mai shekaru 27 zuwa Old Trafford idan ya maye gurbin Erik ten Hag a matsayin kocin Manchester United. (Fichajes Spanish)
Aston Villa na shirin bai wa golan Poland mai shekara 20, Oliwier Zych, sabon kwantiragi, sakamakon zawarcin da Arsenal da Brighton ke masa. (Football Insider)
Barcelona na zawarcin dan wasan River Plate dan kasar Argentina mai shekaru 16 Felipe Esquivel. (Sports Spanish)
Real Madrid na shirin ba wa dan wasan bayan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, kwantiragin fan miliyan 14 zuwa 15 a shekara har zuwa kakar wasa ta 2029-30. (Caught Offside)
Pep Guardiola ya bukaci Manchester City da ta nemi dan wasan baya na RB Leipzig Castello Lukeba, mai shekara 21, inda kocin ke son ganin an dauko dan kasar Faransan a bazara mai zuwa. (Fichajes Spanish)
Barcelona da Arsenal na son dan wasan Colombia mai shekara 20 da ke taka leda a Aston Villa Jhon Duran, sai dai Arsenal ta fi damar daukarsa. (Fichajes Spanish)
A shirye Newcastle take ta saurari tayin da za a iya yi kan dan wasan tsakiyarta dan Ingila Joe Willock mai shekaru 25 a watan Janairu. (Ekrem Konur)










